Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-08 15:22:52    
Hotunan gargajiyya da ci abinci iri iri

cri

Ma'anar hotunan gargajiya da aka zana ita ce a lokacin bikin bazara ta gargajiya wato a kalandar kasar Sin, akan zana hotuna iri iri masu ban sha'awa don manna kan kofoffin gidajen manoma. Da farko an zana wadannan hotuna don magani masifa iri iri,Amma tare da ci gaban zaman al'umma, irin ra'ayin da aka nuna cikin hotuna don magani masifa yana nan yana canjawa sannu a hankali, an kuma gaji da irin hotuna masu al'adar jama'a, yanzu irin hotunan da aka zana suna da ma'ana ta zamani, wato ma'anar hotunan da aka zana ta dace da burin jama'a na yanzu.

Wani gari mai suna Yang liu qin yana shahara a gida da na kasashen waje, domin a wannan wuri mutane da yawa suna iya yin irin hotuna masu kyan gani sosai, kuma dukkansu manoma ne sukan zana hotuna iri iri, wadannan hutunan da ake sayar da su a duk kasar Sin, da farko an sayar da hotunan da manoma na wannan wuri suka zana a arewancin kasar Sin, daga baya mutane na kudancin kasar Sin su ma suna son irin hotuna, domin dukkan hotunan da manoma na gari Yang liu qin suka zana suna sifanta kyakkyawan halin da mutane ke ciki, wato irin abubuwan da aka zana suna shafi zaman yau da kullun na mutanen kasar Sin. An ce, tsawon tarihin hotunan da aka zana sun kai shekaru fiye da dari 3, wato daga shekara ta l6l6 zuwa l9ll na daular Qin ne aka fara zana irin hotuna masu kyan gani sosai. Ma'anar hotunan da aka zana ta kan bayyana tatsuniyoyi iri iri na tarihi. Ban da haka kuma irin hotunan da aka zana wajen kwaikwayo kananan dabobbi da tsuntsaye da shuke shuke da furane iri iri. Wata mallama mai ba da jagora ga ziyararmu ta gaya mana cewa, wani hoto mai halin musamman da aka zana, a kansa ka iya gani hotuna biyu sun hadu, daga wani gefe, ka iya gani hoto daban, daga gaban hoto, ka iya gani wata yarinya take shakatawa a gidan lambun shan iska tana jin dadi sosai.

Bisa abubuwan da aka bayyana cewa, wani halin musamman daban na wannan hoto shi ne daga abubuwan da aka zana cikin hotuna akan iya gane asalin ma'anar hotuna, Misali, in an zana kwado da kifi a kan hoto, wannan yana siffanta za a samu abin alheri da arziki a cikin zaman yau da kullun, Ban da haka kuma, yaran da mutane na garin Yang Liu qin suka zana a kan hutunansu suna da halin musamman, wato dukkan kafoffin yara da suka zana gajere ne kuma masu kiba sosai, kuma kansu manya ne masu ban sha'awa, kuma fuskansu kewaye ne sosai dukkansu suna jawo sha'awar mutane kwarai.

Shin yaya ake yin irin wadannan hutuna masu inganci sosai? Bisa matakai da yawa da za a iya kammala hotunan nan, da farko an saka katako, don kwaikwayo abubuwa iri iri na zaman yau da kullun , sa'an nan za a bi irin dabara da fitar da hotuna iri iri. Wani tsoho mai yin zane ya gaya wa wakilin rediyonmu cewa, daga farkon tsara fasali zuwa yin zane, an yi ayyuka a jere, wato daya bayan daya cikin tsanaki, idan wani aikin da aka yi ba kyau ba, to, ba za a iya zana hotuna da kyau ba,domin wannan aiki yana hade da ayyuka iri iri na fasaha. Ingancin hotunan da aka zana yana da kyau sosai. Yanzu ba ma kawai mutanen kasar Sin suna son saye irin hotuna, har mutane na kasashen waje su ma suna son irin hotuna masu kyau, wato hotunan da aka sayar da su zuwa kasar Rash da Amurka da Japan da Singapore kuma da sauran kasashen duniya. Inda sun samu maraba sosai daga mutane na kasashen waje.

Bayan ka nuna sha'awa ga hotuna, sa'an nan za ka iya dandana abinci iri iri masu dadin ci na birnin Tian jin, a cibiyar birnin Tian jin akwai wani titin musamman, dukkan dakuna na wannnan titi suna sayar da abinci iri iri kawai,, In ka je wannan titi za ka iya ci abinci iri iri na halin musamman na birnin Tianjin.