Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-08 15:16:24    
Birnin Jintan na kasar Sin yana yin kokari domin 'yan makaranta na karkara su iya samun ilmi mai inganci

cri

A cikin wata makarantar karkara wadda ake kiranta "Antou", wakilinmu ya gano cewa, a cikin shekaru biyu da suka gabata, daya bayan daya an kebe kudaden Sin wato Yuan kusan miliyan 8 wajen kyautata sifar makarantar da kayayyakinta da sharudan kafa ta da kuma al'adunta. Ya zuwa yanzu, wannan makaranta ta zo ta gaba a cikin dukkan makarantun lardin Jiangsu a fannin ingancin aikin koyarwa. Kuma He Xiaohe, shugaban makarantar Antou ya bayyana cewa,

"Ingancin aikin koyarwa na makarantar gwaji ta Antou yana ta samun kyautatuwa a 'yan shekarun nan da suka gabata a jere. Yawan 'yan makarantarmu da suka shiga manyan makarantun sakandare a shekara ta 2007 ya kai kashi 90 cikin kashi dari, kuma kusan kashi 40 cikin dari daga cikinsu sun shiga muhimman manyan makarantun sakandare, ta haka mun cimma burinmu na kyautata ingancin aikin koyarwa."

Wan Yuling, wata 'yar makarantar Antou ta gaya wa wakilinmu cewa, tana farin ciki kwarai da gaske da ta iya karatu a wurin, kuma ta ba da imanin cewa, za ta samu maki mai kyau.

"Ana iya samun na'urar sanyaya daki da kyawawan kayayyakin koyarwa a cikin ko wane aji na makarantarmu. Lokacin da muke koyon ilmin kwamfuta, ko wanenmu yana da na'urar kwamfuta guda. Ban da wannan kuma malamanmu sun yi iyakacin kokarinsu wajen koyar mana. Zan gama karatu daga makarantar ba da jimawa ba, kuma ina da imani sosai wajen shiga wata muhimmiyar babbar makarantar sakandare ta lardinmu."

Domin sa kaimi ga saurin bunkasuwar makarantun karkara, birnin Jintan ya shirya harkokin yin cudanya tsakanin malamai na birni da kauyuka. A farkon zangon karatu na lokacin kaka na shekara ta 2007, nagartattun malamai 50 na birnin Jintan da malamai na-gari 50 na kauyuka sun canja ayyukansu. Shugaban hukumar ilmi ta birnin Jintan Li Da ya bayyana cewa,

"wata muhimmiyar alama ta rashin samun daidaito tsakanin makarantun birane da na kauyuka wajen bunkasuwa ita ce rashin samun daidaito tsakanin malaman birane da na kauyuka. Shi ya sa mun bukaci makarantu na-gari na birnin Jintan da su aika da wasu nagartattun malamai zuwa kauyuka don yin aikin koyarwa har shekara guda, ta yadda za a iya kyautata kwarewar malaman kauyuka wajen aiki."

Abin da birnin Jintan ke yi wata shaida ce ta aikin sa kaimi ga bunkasuwar aikin koyarwa na yankunan karkara da wurare daban daban na kasar Sin ke gudanarwa. A nan gaba, kasar Sin za ta ci gaba da kara kebe kudade ga yankunan karkara a fannin ba da ilmin tilas domin dukkan yara na karkara su iya shiga makaranta da kuma samun ilmi mai inganci.(Kande Gao)