Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-08 15:08:59    
Kayayyaki da abubuwa na tarihi sun shaida tarihin kasancewar kabilun Han da Tibet tare a cikin dogon lokacin da ya gabata

cri

A ran 7 ga wata, Mr. Wang Jiapeng wanda ya kware sosai wajen nazarin kayayyaki da abubuwa na tarihi da ke cikin fadar sarkunan kasar Sin ya bayyana cewa, ba ma kawai kayayyaki da abubuwa na tarihi da ake ajiye su a cikin fadar sarkunan kasar Sin suna bayyana huldar da ke tsakanin yankin Tibet da dauloli daban-daban na kasar Sin kai tsaye ba, har ma suna shaida cewa, tun lokacin da, yankin Tibet wani yanki ne da ba za a iya kebe shi daga kasar Sin ba.

Mr. Wang Jiapeng ya bayyana cewa, an ajiye kayayyaki da abubuwa na tarihi masu daraja na yankin Tibet a cikin fadar sarkunan kasar Sin. Ana da mutum-mutumin Buddha irin na zinariya da tagulla fiye da dubu 10 da suke nuna tarihin yankin Tibet. Galibinsu suna da kyau har yanzu, kuma ana da lokacin shigarsu a cikin fadar sarkunan kasar Sin. Bugu da kari kuma, ana da dubban zane-zane na kabilar Tibet, wato Thang-ga a cikin fadar. Wadannan zane-zane na Thang-ga suna bayyana yadda aka yi musanye-musanye a tsakanin kabilar Han da ta Tibet a cikin dogon lokacin da ya gabata.

Mr. Wang Jiapeng ya kara da cewa, a karni na 13 da ya gabata, yankin Tibet ya zama wani yanki na daular Yuan ta kasar Sin a hukunce. A cikin shekaru dari 7 da suka gabata tun daga wancan lokaci, yankin Tibet yana karkashin ikon mulkin gwamnatin tsakiya ta kasar Sin a kullum. Ya zuwa daular Qing, huldar da ke tsakanin kabilar Han da kabilar Tibet ta kara samun karfafuwa sosai. Dalai Lama na zuriya ta 5 da Panchen na zuriya ta 6 da Dalai Lama na zuriya ta 13 sun taba kai ziyara ga sarkunan daular Qing bi da bi. (Sanusi Chen)