A cikin matsalar nuna karfin tuwo da aka yi a ran 14 ga watan Maris a birnin Lhasa, yawan shaguna da kantunan da suka samu lalacewa ya kai 908. Bayan da aka musu gyara, yanzu shaguna da kantuna fiye da dari 5 sun sake bude kofofinsu.
An labarta cewa, lokacin da zaman al'ummar birnin Lhasa ya samu kwanciyar hankali, yanzu ana gaggauta aikin gyara kantuna da shagunan da suka samu lalacewa mai tsanani a cikin matsalar, kuma za su bude kofa a nan gaba ba da dadewa ba. (Sanusi Chen)
|