Za a sake maido da sha'anin yawon shakatawa na jihar Tibet mai cin gashin kai ta kasar Sin daga ran 1 ga watan Mayu na shekarar da muke ciki.
Mr. Tanor, mataimakin shugaban hukumar yawon shakatawa ta jihar Tibet ya bayyana cewa, a lokacin, kamfanonin yawon shakatawa daban daban za su tattara kungiyoyin masu yawon shakatawa na gida da na waje wajen shiga jihar Tibet don yin ziyara, haka kuma mutanen da suke yawon shakatawa da kansu su ma za su iya shiga jihar Tibet don ziyara lami lafiya. Yanzu hukumomin yawon shakatawa na jihar suna namijin kokari wajen gudanar da ayyukan share fage don sake bude wuraren shan iska.(Kande Gao)
|