Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-01 20:10:08    
Jihar Tibet, wani bangare ne na kasar Sin har abada

cri
Ran 1 ga wata, kamfanin dillancin labaru na Xinhua, wanda shi ne mafi yin girma a kasar Sin, ya ba da wani sharhi da cewa, a can da, kuma a yanzu, kuma a nan gaba, jihar Tibet, wani bangare ne da ba a iya raba shi daga kasar Sin ba.

Sharhin ya bayyana cewa, a ran 14 ga watan Maris, an yi tashe-tashen hankula a birnin Lhasa, babban birnin jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin. Mutane sun gano ainihin burin rukunin Dalai Lama na neman kawo wa kasar Sin baraka.

Sharhin ya ci gaba da cewa, a zamanin daular Yuan, wato yau da shekaru fiye da 700 da suka wuce, yankin Tibet ya zama wani bangare na kasar Sin a hukunce. Sarakunan zamanin da na Sin sun yi ta mulkin yankin Tibet. Bayan kafuwar sabuwar kasar Sin a shekarar 1949, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin da wakilan hukumar yankin Tibet sun rattaba hannu kan jerin yarjejeniyoyi kan 'yantar da jihar Tibet cikin lumana. A shekarar 1965 jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin ta kafu. Abubuwan gaskiya sun nuna cewa, tun can da har zuwa yanzu jihar Tibet, wani bangare ne da ba a iya kebe shi daga kasar Sin ba.(Tasallah)