Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-01 19:45:50    
Kakakin kasar Sin ta yi jawabi kan wasikar da Dalai Lama ya aika zuwa ga dukkan Sinawa

cri
Ran 1 ga wata, a nan Beijing, madam Jiang Yu, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta yi jawabi kan wasikar da Dalai Lama ya aika zuwa ga dukkan Sinawa a duniya.

Madam Jiang ta bayyana cewa, a cikin shekaru kusan 50 da suka wuce, rukunin Dalai Lama yana canza tarihi da ta da rikici a tsakanin al'ummomi da kuma lalata kwanciyar hankali na zaman al'ummar kasar Sin domin neman 'yancin kan Tibet. A kwanan baya, rukunin Dalai Lama ya zuga da kuma shirya tashe-tashen hankula a birnin Lhasa da sauran yankunan Tibet, wadanda suka kawo wa jama'a babbar illa ta fuskar rayuka da dukiyoyi, shi ya sa jama'ar kasar Sin 'yan kabilu daban daban suka nuna matukar fushi, haka kuma, kasashen duniya sun yi tir da wadannan tashe-tashen hankula. Tashe-tashen hankulan sun sake nunawa kasashen duniya ainihin halin Dalai Lama, wanda ya kan yi shelar kin yarda da nuna karfin tuwo. Shaidun da ba a iya musunta ba sun shaida cewa, Dalai Lama ya yi yunkurin bayar da wata wasika wadda take cike da karya domin wanke kansa daga tashe-tashen hankula da suka faru a Lhasa, amma ba zai sami nasara ba.

Kazalika kuma, madam Jiang ta kara da cewa, a wani bangare, Dalai Lama ya yi shelar yin tattaunawa da tuntubar gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, a waje daya kuma, ya ta da tarzoma a kasar Sin, ya kawo cikas ga gasar wasannin Olympic ta Beijing da jama'a da 'yan wasa na kasashen duniya suke zura ido a kai, ya raunana tushen yin tattaunawa sosai. In Dalai Lama ya yi shirin yin tattaunawa da tuntubar gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, kuma ya amince da kasancewar jihar Tibet a matsayin wani bangare na kasar Sin, to, ya kamata ya daina zuga tayar da dukkan tashe-tashen hankula nan da nan, ya daina kawo illa da cikas ga gasar wasannin Olympic ta Beijing, ya kuma daina dukkan aikace-aikacen neman kebe jihar Tibet daga kasar Sin.(Tasallah)