An labarta cewa, hadaddiyar kungiyar Sinawa 'yan kaka-gida ta duniya ta shirya wani taron tattaunawa kwanan baya ba da dadewa ba a nan birnin Beijing domin yin Allah wadai da kakkausan harshe da lamarin ' 3.14' da ya auku a Lhasa da kuma aika-aikan da wassu mutane masu neman samun 'yancin Tibet suka yi na kai farmaki ga ofisoshin jakadancin kasar Sin dake ketare.
Babban sakataren hadaddiyar kungiyar Mr. Ren Xinglian ya furta cewa, hakikanan abubuwa sun shaida cewa, gungun mutane mabiya Dalai Lama ne suka kulla makarkashiyar haddasa lamarin " 3.14 '' da zummar shuka barna ga yunkurin mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics da kuma yin zagon kasa ga tsari da oda na birnin Lhasa. ( Sani Wang )
|