Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-31 20:18:40    
Jita-jitar da Dalai Lama ya ji ba za ta iya canja hakikanan abubuwa ba

cri
A ran 31 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Jiang Yu ta bayyana a nan birnin Beijing, cewar jita-jitar da Dalai Lama ya ji ba za ta iya canja hakikanan abubuwan da suka auku ba.

Wani dan jarida ya yi tambaya cewa, a kwanan baya, a gun wani taron manema labaru da aka shirya a birnin New Dheli na kasar Indiya, Dalai Lama ya musunta goyon bayan da ya nuna wa tashin hankalin da aka tayar a birnin Lhasa, har ya ce, ya ji an ce, an tayar da wannan tashin hankali ne sabo da daruruwan sojojin kasar Sin su sanya tufafin 'yan Buddha.

Jiang Yu ta ce, kowa ya sa hakikanan abubuwa na tashin hankali da aka yi a Lhasa, abubuwan shaidu suna kasancewa a nan duniya, kuma ba a iya canja su ko kadan ba. Jita-jitar da Dalai Lama ya ji ba gaira ba dalili ba su iya canja hakikanan abubuwan da suka auku ba. Sai dai ya shaida cewa, babu sauran hanyar da Dalai Lama zai iya zaba, sai ya yi amfani da jita-jita domin kubutar da kansa daga matsalar tayar da laifuffuka da aka yi a Lhasa. (Sanusi Chen)