Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-31 17:18:26    
Ba shakka bacewar al'adun Tibet a bakin rukunin Dalai Lama karya ce

cri
Tenzin Chepa, masani kan ilmin kabilar Tibet da ya taka muhimmiyar rawa a cikin jerin ayyukan ceto da kiyaye al'adun gargajiya na kabilar Tibet ya bayyana cewa, ba shakka bacewar al'adun Tibet a bakin rukunin Dalai Lama karya ce.

Ya bayyana cewa, daga shekara ta 1986, daya bayan daya jihar Tibet mai cin gashin kai ta kasar Sin ta tattara da wallafawa da kuma buga 'Babi na jihar Tibet daga cikin littafin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin' da 'Babi na Tibet daga cikin littafin wake-wake na gargajiya na kasar Sin' da kuma littattafai kan raye-raye na gargajiya da karin magana da wasannin kwaikwayo na gargajiya da wakokin gargajiya na almara da dai sauransu, ta haka an ceto da kuma kiyaye nagartattun al'adun gargajiya na kabilar Tibet sosai.

Littafin Addinin Buddh da aka rubuta da harshen Tibet yana kunshe da shahararrun littattafai fiye da 4000 na addinin. Mr. Tanzin Chepa ya bayyana cewa, kasar Sin ta kebe kudaden Sin wato Yuan kusan miliyan 40 don yin gyare-gyare gare shi. Kuma ana sa ran cewa, za a kammala wannan aiki a karshen shekara mai zuwa.(Kande Gao)