Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-30 17:22:55    
Ba a iya musunta cigaban da aka samu wajen kyautata zaman rayuwar jama'ar Tibet ba

cri
A ran 29 ga wata, jaridar "Economic Daily" ta kasar Sin ta buga wani bayani mai take "ba a yarda da a musunta cigaban da aka samu awjen kyautatuwar zaman rayuwar jama'ar Tibet ba" da aka rubuta bayan da aka kai ziyara ga Mr. Xia Chuntao, wani masanin da ke aiki a cibiyar nazarin ilmin zaman al'ummar kasar Sin da Mr. Zhaluo, wani dan kabilar Tibet wanda ke nazarin kabilun kasar Sin.

Mr. Xia ya ce, a cikin shekaru fiye da 50 da suka gabata bayan da aka 'yantar da jihar Tibet cikin lumana, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta mai da hankali sosai a kullum kan tallafawa jihar wajen neman cigaban tattalin arziki da zaman al'ummar jihar. Ta kuma tsara manufofi masu gatanci da yawa da suke moriyar cigaban tattalin arziki da al'adu da ilmi da likitanci da fasaha da kimiyya da cinikayya a jihar. Sabo da haka, jihar Tibet ta samu cigaba cikin sauri sosai. Zaman rayuwar jama'arta ma ya samu kyautatuwa kwarai. (Sanusi Chen)