Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-28 21:49:41    
Yadda hukumar jihar Tibet mai cin gashin kanta ta daidaita tarzomar Lhasa ya sami fahimta da goyon baya daga gamayyar kasa da kasa

cri
Game da tarzomar da ta auku a ranar 14 ga wata a birnin Lhasa, hedkwatar jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin, kwanan nan, kasashe daban daban, ciki kuwa har da Afirka ta tsakiya da Peru da Thailand da dai sauransu sun bi hanyoyi daban daban wajen nuna goyon bayansu ga yadda bangaren Sin ya daidaita mummunar tarzomar Lhasa, kuma sun yi fatan za a maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Tibet tun da wuri.

shugaban ofishin fadar shugaban kasar Afirka ta tsakiya kuma ministan harkokin gida na kasar, Gbezera ya bayyana cewa, 'yan awaren Tibet sun tayar da tarzoma a birnin Lhasa a kan yunkurin jawo wa kasar Sin baraka, kuma tabbas ne za su ci tura. Tibet wani kashi ne na kasar Sin wanda ba za a iya raba shi ba, kuma gwamnatin Afirka ta tsakiya na tsayawa kan bin manufar Sin daya tak a duniya.

Ya zuwa yanzu, kasashe da kungiyoyin duniya da yawansu ya kai 120 sun bi hanyoyi daban daban wajen nuna fahimtarsu da goyon bayansu ga matsayin adalci na kasar Sin.

Bayan haka, kwanan nan, masu sauraron rediyon kasar Sin ma sun bugo mana waya ko turo mana wasiku, inda suka yi Allah wadai da aukuwar tarzoma a birnin Lhasa da babbar murya.(Lubabatu)