Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-28 20:50:04    
Kasar Sin ta tabbatar da hakkin zaman rayuwa da na samun bunkasuwa na jama'ar jihar Tibet

cri

A ran 28 ga wata, kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin ya bayar da wani labari, inda ya bayyana cewa, a cikin kusan shekaru 50 da suka gabata, wato bayan da aka yi gyare gyare kan dimokuradiyya a jihar Tibet da ke da ikon tafiyar da harkokin kanta, kasar Sin ta tabbatar da hakkin zaman rayuwa da na samun bunkasuwa na jama'ar jihar Tibet yadda ya kamata.

A 'yan shekarun baya, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai da yawa, domin taimakawa jihar Tibet da ta samun saurin bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma. A halin yanzu dai, jihar Tibet tana cikin zamanin da ya fi kyau a tarihi wajen samun bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma, yawan karuwar tattalin arzikinta ya fi matsakaicin matsayin kasar Sin yawa a cikin shekaru da dama.

Kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya ce, tarihin jihar Tibet mai tsawon kusan shekaru 50 ya nuna wa duniya cewa, idan ana tsayawa kan hanyar gurguzu da ke da abubuwan musamman na kasar Sin, idan ana tsayawa kan tsarin tafiyar da harkokinsu da kansu a yankunan kananan kabilu, jihar Tibet za ta iya samun wata kyakkyawar makoma.(Danladi)