Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-28 16:59:08    
Nufin gaskiya na 'hanyar tsaka-tsaka' da rukunin Dalai Lama yake bi shi ne samun 'yancin kai na Tibet

cri

A ran 28 ga wata, kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya bayar da wani sharhin edita cewa, nufin gaskiya na 'hanyar tsaka-tsaka' da rukunin Dalai Lama yake bi shi ne samun 'yancin kai na Tibet.

Sharhin ya ce, a 'yan shekarun baya, rukunin Dalai Lama ya kan sanar da ra'ayinsa na 'hanyar tsaka-tsaka' ga kasashen duniya, wato ya ce, bisa kundin tsarin mulkin kasar Sin ne, rukunin Dalai Lama yake neman cimma burin 'tafiyar da harkokinsu da kansu, da tafiyar da mulkinsu a hakika' a jihar Tibet da sauran yankunan da 'yan kabilar Tibet suke zama. Amma idan aka yi nazari kadan, ana iya ganin cewa, hakikanin abu na 'hanyar tsaka-tsaka' ba shi da bambanci da samun 'yancin Tibet, dukkansu suna son kawo barakar Tibet daga kasar Sin.

Wannan sharhin edita ya ci gaba da cewa, ba za a iya cin nasarar samun 'yancin Tibet ba, ba za a iya bin 'tsakiyar hanya' cikin nasara ba. Wata kyakkyawar makoma ga rukunin Dalai Lama ita ce, ya yi watsi da ra'ayin samun 'yancin Tibet, da daina gudanar da ayyukan kawo baraka ga kasar Sin, da kuma yi ban kwana da mafarkinsa na da.(Danladi)