Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-27 16:22:38    
Ya kamata rukunin Dalai Lama ya sa aya ga surutunsa na bacewar al'adun Tibet

cri
A ran 26 ga wata, kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin ya ba da sharhi, inda ya nuna cewa, ya kamata rukunin Dalai Lama ya sa aya ga surutunsa na bacewar al'adun Tibet.

Sharhin ya bayyana cewa, kafin a yi gyare-gyaren demokuradiyya a jihar Tibet mai cin gashin kai ta kasar Sin, bayin da yawansu ya kai kashi 95 bisa kashi dari daga cikin dukkan 'yan jihar ba su da hakkin rayuwa balle ma hakkin more al'adu. A cikin shekaru kusan 50 da suka gabata bayan da aka yi gyare-gyaren demokuradiyya, al'adun Tibet sun samu sabon ci gaba bisa tushen gadon abubuwan gargajiya da kuma kiyaye halayen musamman na kabilar Tibet. Ba kawai an canja halin da jihar ta sami kanta a ciki wanda tsirarun masu mallakar bayi suka yi babakere da al'adun Tibet, har ma aka sanya jama'ar Tibet suna iya gado da rayawa da kuma more al'adun Tibet tare.

Wasu kwararru kan batun Tibet suna ganin cewa, dalilin da ya sa rukunin Dalai Lama ya yada karyarsa a ko ina kan cewa, wai al'adun Tibet sun gushe shi ne sabo da yana son sa kaimi ga wasu rukunonin siyasa na kasashen yamma da suke dora matukar muhimmanci kan hakkin bil Adama domin su kai wa kasar Sin matsin lamba, ta yadda zai iya cimma burinsa na neman kawo wa kasar Sin baraka.(Kande Gao)