Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-27 13:27:02    
Kungiyar manema labaru ta kasar Sin ta yi kakkausar suka ga wasu kafofin yada labaru na kasashe yammacin duniya da suka bayar da rahotannin karya kan lamarin Lhasa

cri
Kwanakin nan, kungiyar manema labaru ta kasar Sin ta ba da sanarwar, inda ta yi kakkausar suka ga wasu kafofin yada labaru na  kasashen yammacin duniya da suka murda gasikiya da bayar da rahotannin karya kan tashen-tashen hankula da suka hada da duke-duke da fasa abubuwa da kwashe kayayyaki da cunnawa wurare wuta da suka faru a birnin Lhasa a ran 14 ga watan Maris

A cikin sanarwar, an bayyana cewa, wasu kafofin yada labaru na kasashen yammacin duniya masu mummunar manufa sun bayar da rahotannin son zuciya kan lamarin Lhasa, wanda ta keta ka'idar manema labaru daga tushensu. Misali, wasu kafofin yada labaru na kasashen yammacin duniya masu mummunar manufa sun yi amfani da fasahar sarafa hoto ta PS wajen kyautata hotuna. Wasu muhimman kafofin yada labaru sun gyara adadi yayin da suka bayar da rahotanni, kuma sun kara gishiri kan lamarin da ya faru a Lhasa. Sun bayyana cewa wai "daruruwan mutane sun raunata", kuma "an yi kisan gilla ga daruruwan mutane". Haka kuma sun baza wadannan jita-jita a tsakanin jama'a.

A cikin sanarwar, an bayyana cewa, kullum kungiyar manema labaru ta kasar Sin tana dora muhimmanci sosai wajen inganta ka'idar manema labaru, kuma sun yi kokari ba tare da kasala ba. Amma, yayin da wasu takwarorinmmu na kasashen ketare suka bayar da rahotanni kan lamarin Lhasa, sun keta ka'idar manema labaru, ba su bayar da hakikanan abubuwa da suka faru cikin gaskiya da kuma adalci ba. Kungiyar manema labaru ta kasar Sin ta yi kakkausar suka kan lamarin.(Bako)