Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-26 16:50:01    
Shugabannin jam'iyyun wasu kasashe sun nuna goyon baya ga Sin da ta daidaita tarzomar Lhasa bisa doka kuma yadda ya kamata

cri
Kwanan nan, shugabannin jam'iyyun kasashen Rasha da Brazil da Samoa da Masar da Mauritania da Fiji da Iraki da Palasdinu da Indiya da dai sauransu sun bayyana cewa, suna nuna goyon baya ga Sin da ta daidaita mummunar tarzomar da ta auku a birnin Lhasa bisa doka.

Shugaban kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta tarayyar Rasha kuma dan majalisar dokokin kasar, Gennadi Zuganov ya bayar da sanarwa, inda ya yi nuni da cewa, tarzomar da aka samu a birnin Lhasa makarkashiya ce da aka kulla kan yunkurin adawa da kasar Sin, kuma jam'iyyar kwaminis ta Rasha na nuna tsayayyen goyon baya ga matakan da shugabannin Sin suka dauka wajen dakile laifuffukan, kuma tana Allah wadai da mayar da wasannin Olympics a siyance da wasu ke yi.

Bayan haka, shugabannin kasashen Brazil da Samoa da Masar da Palasdinu da Mauritania da Fiji da Iraki da Indiya da Singapore su ma sun la'anci tarzomar da ta auku a Tibet, sun kuma nuna goyon baya ga kokarin da gwamnatin kasar Sin da jama'arta suke yi wajen kwantar da tarzomar.(Lubabatu)