Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-25 16:48:19    
Me ya faru a Lhasa, a idanun masu yawon shakatawa na yammacin duniya

cri
A lokacin da 'yan Tibet da mabiyansu suke yin zanga-zanga a duk duniya domin nuna kin yarda da wai gwamnatin kasar Sin ta kwantar da kura a birnin Lhasa, babban birnin jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin a kwanan baya, a ran 18 ga wata da dare, jaridar The Daily Telegraph ta Birtaniya ta ba da labari mai lakabi haka ''yan Tibet sun duka 'yan kabilar Han, in ji masu yawon shakatawa da ke ziyara a Lhasa', inda wasu masu yawon shakatawa na kasashen yammacin duniya suka yi bayani kan yadda tarzoma ta wakana a Lhasa a idanunsu.

Labarin ya ce, wadannan masu yawon shakatawa na kasashen yammacin duniya sun isa birnin Kathmandu, hedkwatar kasar Nepal ba da dadewa ba bayan da suka tsere daga Lhasa, wanda aka riga aka yi masa kawanya. Sun bayyana cewa, a ran 14 ga wata, sun ga yadda masu bin addinin Buddha na jihar Tibet cikin fushi suke dukan 'yan kabilar Han.

Claude Balsiger mai shekaru 25 da haihuwa da ya zo daga kasar Sweden ya bayyana cewa, ya ga yadda tashin hankali ya faru a babban filin Barkhor a kusan da gidan ibada na Jokhang a Lhasa. Ya waiwayi abubuwan da suka faru a gaban idonsa, ya ce, matasa sun ta da tarzoma, tsofaffi kuwa suna yin ihu domin nuna musu goyon baya. Muryar tsofaffin ta yi kama da kukan kura. Ya kara da cewa, ga alamar cewa, 'yan kabilar Han ne kawai aka kai wa hare-hare. An jefa wa 'yan kabilar Han a kalla 7 ko kuma 8 duwatsu, an kuma duke su da hannu. Sa'an nan kuma, wasu tsofaffi 'yan kabilar Tibet sun kubutar da wani tsoho dan kabilar Han daga masu bin addinin Buddha. An ce, wani mai yawon shakatawa ya kubutar da wani dan kabilar Han daban saboda ya shiga tsakani.

Bugu da kari kuma, wani mai yawon shakatawa daban, wato John Kenwood mai shekaru 19 da haihuwa da ya zo daga kasar Canada ya gane wa idonsa mutuwar wani dan kabilar Han a sakamakon hare-haren da 'yan Tibet suka kai masa. Mr. Kenwood ya ce, wani mutum yana kan babur yana wucewa, amma suka yi ta dukansa, har ya fado daga babur dinsa. Ban da wannan kuma, an y ta jefar kan wani mutum da babban dutse a gefen hanya. Bayan da masu kai hare-haren suka bar shi, wannan mutum bai motsa ba.

Kazalika kuma, Mr. Kenwood ya ga an samar wa 'yan Tibet masu tarzomar akwatuna da dama, wadanda cike suke da duwatsu, ta haka masu tarzomar suka iya kai wa 'yan kabilar Han hare-hare. A ganin Mr. Kenwood, abun da ya faru a gaban idonsa ya yi kama da wani abun da aka gudana bisa shirin da aka tsara. Wasu masu yawon shakatawa 2 daban sun yi bayani da cewa, a ran nan, an yi ta yada jita-jita da cewa, wai 'yan kabilar Han sun kashe wasu masu bin addinin Buddha da aka kama su. Irin wannan jita-jita ta karfafa fushin masu tarzomar.

Mr. Kenwood ya waiwaya ya kuma ci gaba da cewa, bayan da aka kawo karshen tashe-tashen hankula a wannan rana, ya ga hasken wuta a kan wasu gine-gine a Lhasa, haka kuma, akwai hayaki a ko ina a birnin. Bai taba yin tsammani da cewa, masu bin addinin Buddha za su ta da tashe-tashen hankula kamar hakan ba.(Tasallah)