Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-25 11:34:57    
'Yan sanda na kasar Sin sun kama mutane masu yin laifuffukan sa wuta a cikin al'amarin Lhasa da ya faru a ran 14 ga watan Maris

cri

A cikin shirinmu na yau za mu yi muku bayani dangane da 'yan sanda na kasar Sin sun kama mutane 2 masu yin laifuffukan sa wuta a cikin al'amarin ta da hankali a cikin birnin Lhasa na jihar Tibet ya faru a ran 14 ga watan Maris.

Ran 24 ga wata, a gun taron manema labaru da ma'aikatar zaman tsaro na jama'a ta kasar Sin ta yi, an sanar da cewa, 'yan sanda na kasar Sin sun ria sun cafke gungun masu laifin kone kone, sun kama dukkan mutane 5 masu taka laifuffukan sa wuta. Madam Shan Huimin kakaki ta ma'aikatar ta nuna cewa, yanzu an riga an sami kwanciyar hankali kan al'amarin Lhasa. Yayin da 'yan sanda da sojojin tsaro suke warware al'amarin, sun yi matukar hakuri sosai, ba su yi amfani da ko wane irin munanan makamai ba.

A ran 14 ga watan Maris, an sami al'amarin ta da manyan laifuffuka masu tsanani sosai a cikin birnin Lhasa na jihar Tibet. A cikinsu, mutane masu yawa wadanda ba su ji ba ba su gani ba sun mutu ko jikkata a sakamakon laifuffukan sa wuta a kantin tufafi na Yichun da sa wuta a kantin mota na garin Dagze da aka yi. Madam Shan Huimin ta yi bayani kan labarin kama mutane masu yin laifuffukan. Ta ce,

"A kwanakin baya, bi da bi ne 'yan sanda na birnin Lhasa sun kama mutane 3 masu yin laifin sa wuta kan 'kantin tufafin Yichun' da mutane 2 masu yin lafin sa wuta kan 'kantin mota na garin Dagze'.bayan tuhuma ta farko da aka yi, masu yin laifuffuka sun amsa laifuffukansu."

An bayyana cewa, a ran 14 ga wata da yamma da karfe 2 da rabi, Qime Lhazom da Ben'gyi da sauran wani mutum sun shiga "kantin tufafi na Yichun", sun kyasta wuta kan tufafi har sau uku, sai kanti ya kama gobara, bayan haka, sun bar wurin. Akwai cikakken abubuwan shaidu sun shaida cewa, su uku sun yi laifi a "kantin tufafi na Yichun", kuma wannan gobara ta kashe ma'aikata 5 na kabilar Han da Tibet.

An yi laifin sa wuta daban a ran 15 ga wata da karfe 10 da yamma. Loyar wanda ya shiga aikace-aikacen ta da hankali a garin Dagze ya kyasta wuta kan wani kanti, bayan haka, ya je kantin mota, ya karye kofa tare da sauran wani mutum mai suna Kangzug, sun sa wuta a wannan kanti. Ban da haka kuma sun jefa tukwanen gas biyu cikin wuta, wannan ya haddasa mutane 5 da suke boye a cikin kanti sun mutu, a cikinsu akwai mata da miji, da wani 'dansu wanda shekarunsa watanni 8 kawai, da ma'aikata biyu.

A gun taron manema labaru, an nuna Video da aka dauka yayin da ake binciken mahalli, kallon wannan abin takaici ne. Madam Shan Huimin ta nuna cewa,

"Aikace-aikacen da wadannan mutane 5 da aka gabata sun riga sun karya dokar kasar Sin. Abin gaskiya ya fi ko wace irin magana.wannan ya sake shaida cewa, al'amarin da ya faru a ran 14 ga watan Maris, ko shakka babu ba wai 'zanga-zanga mai kwanciyar hankali' ko 'nuna rashin jin dadi ta hanyar zaman lafiya' ba, a gaskiya shi ne al'amarin tada manyan laifuffuka mai tsanani sosai." Bisa amsar da masu yin laifuffuka suka yi, tashin hankali da ya faru a Lhasa, harkar shuka barna ce da rukunin Dalai Lama ya shirya. Madam Shan Huimin ta ce, "Burinsu shi ne haifar da tarzoma, da kuma ba da mugun tasiri ko lalata wasannin Olympics na Beijing, da kuma bata kyakkyawan hali mai zaman karko da hadin kai na kasar Sin, ta haka domin neman ballewa daga kasa. Aikaci-aikacen da gungun masu kone kone suka yi su sami rashin jin dadi daga mutanen kabilu dabam daban na jihar Tibet."

Bayan al'amarin ya faru, nan da nan gwamnatin jihar Tibet ta dauki matakai yadda ya kamata. Yanzu, an riga an sami kwanciyar hankali, an sami oda yadda ya kamata a birnin Lhasa. Madam Shan Huimin ta nuna cewa,

"Yayin da hukumar zaman tsaron jama'a suke tafiyar da ayyukansu, kullum suna tsayawa tsayin daka kan ka'idojin kiyaye zaman karko, da kiyaye oda ta doka, da kiyaye babbar moriyar jama'a. kuma ba su yi amfani da ko wane irin munanan makamai ba."

Bisa labarin da muka samu, wannan al'amarin ya haddasa 'yan sanda da sojojin tsaro 242 sun jikkata, sauran wani ya rasu. Ya zuwa yanzu, ana cigaba da yin tuhuma kan wadannan laifuffukan sa wuta biyu.