Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-25 10:00:52    
Wasu kafofin yada labaru na kasashen duniya sun yada hakikanan labaru kan lamarin da ya auku a birnin Lhasa

cri
A ran 19 ga wata, shafin yanar gizo na Australia ya bayar da wani dogon bayani mai lakabi haka, "masu yawon shakatawa sun ga yadda aka da da kashi wa mutanen kabilar Han". A cikin wannan bayani, an ce, wasu masu yawon shakatawa na kasashen yammacin duniya wadanda suka bar tsaunin Himalayas sun bayyana cewa, a ranar da aka ta da zaune tsaye a birnin Lhasa, matasan Tibet mahaukata sun yi ta jifar 'yan kabilar Han da duwatsu, tare da yi wa 'yan kabilar Han duka, kuma sun kone shagunansu.

A ran 18 ga wata, Mr. Ken Wood, wani dan kasar Canada da sauran masu yawon shakatawa wadanda suka dauki jirgin sama suka isa birnin Kathmandu na kasar Nepal sun ga yadda aka ta da zaune tsaye a ranar Jumma'a, wato ran 14 ga watan Maris da idanunsu. Mr. Ken Wood ya ce, "Wannan matsala ce mai tsanani da aka shirya wa 'yan kabilar Han da musulmai". Wannan matsala ce ta nuna karfin tuwo da ta shafi birnin Lhasa gaba daya.

Wadannan masu yawon shakatawa na kasashen yammacin duniya sun almanta cewa, 'yan ta'adda sun yi duka wa 'yan kabilar Han da hannayensu da kafafunsu gaba daya ba tare da tausayi ko kadan ba. 'Yan Tibet sun zargi wadannan 'yan kabilar Han wadanda suka shiga yankin Tibet da cewa suna canja al'adun musamman na Tibet da hanyar zaman rayuwarsu. Mr. Ken Wood ya ce, ya ga wasu 'yan Tibet suna dukan wani dan kabilar Han wanda ke kan babur da duwatsu da kafafunsu. "Daga karshe dai sun duke shi sanda ya kwanta a kasa, sannan suka duke shi a kansa da duwatsu har ya rasa, kuma bai ko motsa ba."

Mr. Ken Wood ya ce, "ina tsammani wannan saurayi dan kabilar Han ya mutu." Amma jim kadan, Mr. Ken Wood ya kara da cewa, bai iya tabbatar da wannan ba. Amma Ken Wood ya tabbatar da cewa, bai ga wani dan Tibet da ya mutu a birnin Lhasa a cikin wannan matsala ba.

Shafin yanar gizo na Australiya ya nuna cewa, a ran 18 ga wata, wai gwamnatin Tibet wadda ke gudun hijira ta tabbatar da cewa, a cikin hargitsin da aka yi har na tsawon fiye da mako daya, 'yan Tibet 99 sun mutu sabo da duka da aka musu. Amma gwamnatin kasar Sin ta jaddada cewa, fararen hula 13 ne suka mutu sakamakon wannan hargitsi. Kuma lokacin da take kwantar da kura a Lhasa, ba ta yi amfani da kowane irin makamin da zai iya kashe mutum ba.

Mr. Ken Wood ya alamanta cewa, a wuraren da 'yan Tibet suka wuce, sun jefa duwatsu kan kayayyakin da suka gani. "Sun kai farmaki kan wani tsoho, dan kabilar Han wanda ke kan keke. Sun jefe shi da duwatsu. Wasu tsofaffi 'yan kabilar Tibet sun fito sun yi kokarin hana su", a cewar Ken Wood.

Wannan mai yawon shakatawa da ya zo daga kasar Canada ya waiwayi wani labarin ceto daban. Ya ce, wani dan kabilar Han yana rokon 'yan Tibet wadanda suke yi masa barazana da duwatsu. "Sun harbe hakarkarinsa da kafafunsu, jini ya gudana kan fuskarsa duka. A wannan lokaci, wani Bature ya zo ya tayar da wannan dan kabilar Han. 'Yan Tibet wadanda suke da duwatsu a cikin hannayensu sun kewaye su biyu. Wannan Bature ya taimaki wannan dan kabilar Han, ya kada hannunsa ga sauran mutane. Daga karshe dai, 'yan Tibet sun yarda da ya kai wannan dan kabilar Han a wani wurin kare lafiyarsa."

Game da abubuwan da masu yawon shakatawa na kasashen yammacin duniya suka almanta, Thubten Samphel, wai kakakin gwamnatin Tibet wadda ke gudun hijira ya ce, wannan hargitsin nuna karfin tuwo hargitsi ne mai ban tausayi sosai. Ya kuma ce, "a kullum an nemi 'yan Tibet da su yi gwagwarmaya ba tare da nuna karfin tuwo ba."

A waje daya kuma, shafin yanar gizo na Australiya ya nuna cewa, a rana ta biyu bayan aukuwar hargitsin nuna karfin tuwo a Lhasa, wato ran 15 ga watan Maris, rundunar tabbatar da kwanciyar hankali ta kasar Sin ta rufe yankin Lhasa. Sun nemi masu yawon shakatawa da su zauna a cikin otel-otel da suke kwana. Amma a ran 17 ga wata, sun yarda da masu yawon shakatawa su fito su yi yawo a cikin birnin Lhasa. Amma dole ne su nuna fasfot nasu a tasoshin bincike.

Mr. Serge Lachapelle wanda ya zo daga Montreal na kasar Canada ya tuna da abubuwan da ya gani a wancan rana, cewar "an kone shaguna da yawa a birnin Lhasa. An kone kusan dukkan shagunan da ke gefunan tituna. An kuma lalata gine-gine da yawa."

Mr. Ken Wood ya kuma ce, "an rushe kusan dukkan yankunan musulmi. An kuma lalata dukkan shagunansu". "Jiya, wato ran 17 ga wata da safe, na iya fitowa daga otel na ci abinci a waje. Amma ban iya ganin murmushi a kan fuskar 'yan Tibet ba."  ?Sanusi Chen?