Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-24 16:02:58    
Tashar internet ta gidan telebijin na RTL na kasar Jamus ta amince da bayar da labarai marasa gaskiya game da lamarin nuna karfin tuwo a jihar Tibet ta kasar Sin

cri

A ran 23 ga wata, tashar internet ta gidan Telebijin na RTL na kasar Jamus ta bayar da wata sanarwa a shafin internet, inda ta amince da bayar da labarai marasa gaskiya game da lamarin nuna karfin tuwo a jihar Tibet ta kasar Sin.

A 'yan kwanakin baya, tashar internet ta gidan telebijin na RTL ta bayar da wani hoto, inda 'yan sanda 4 suka kori masu zanga zanga da sandarsu, kuma aka bayyana cewa, ' 'yan sanda na kasar Sin suka murkushe masu zanga zanga a Tibet.' A ran 23 ga wata, wannan tashar internet ta amince da kuskurenta, a hakika dai, abin da wannan hoto ya nuna shi ne, 'yan sanda na kasar Nepal suna korar masu zanga zanga a birnin Kathmandu, babban birnin kasar. Sabo da haka ne, wannan tashar internet ta amince da kuskurenta, kuma ta nuna bakin ciki game da haka.(Danladi)