Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-24 12:36:38    
Ba za a iya murde gaskiya ba kuma adalci yana zukatan jama'a

cri

Ran 23 ga wata, kamfanin dilancin watsa labaru na Xinhua na kasar Sin ya bayar da wani sharhi kan wasu kafofin watsa labaru na kasashen Turai da suka murde gaskiya kan al'amarin ta da manyan laifuffuka masu tsanani sosai da suka faru a cikin birnin Lhasa na lardin Tibet, sharhin ya yi nuni da cewa, ba za a iya murde gaskiya ba kuma adalci yana zukatan jama'a.

A cikin wannan sharhi, an ce, bayan lamarin tada manyan laifuffuka masu tsanani a birnin Lhasa na lardin Tibet, wasu kafofin watsa labaru na kasashen Turai sun bayar da rahotani a jere wadanda suka murde gaskiya kan al'amarin Lhasa, kuma sun yi suka ga matakin da gwamnatin kasar Sin ta dauka da manufar da take tafiyarwa a jihar Tibet, sun yi zargin wai gwamnatin kasar Sin ta "kwace 'yancin bin adinai na mutanen Tibet", kuma sun dakushe kwarjinin gasar wasannin Olympics ta Beijing.

Wannan sharhi ya yi nuni da cewa, ba za a iya murde gaskiya ba kuma adalci yana zukatan jama'a. Manofofi da matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka ya sami goyon baya da fahimmta daga fannonni masu yawa. Kasashe da kungiyoyi fiye da 100 na duniya sun nuna goyon baya kuma jama'ar Tibet suna tsayawa bangaren hadin kai da zaman karko.