Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-24 10:29:41    
Wani dan Amurka ya ce zai koma birnin Lhasa don aiki a wata mai zuwa

cri

Wakilin wata shahararriyar jaridar Singapour ya ruwaito daga Beijing a ran 20 ga wata cewa, wani dan Amurka da ya taba fama da tarzomar birnin Lhasa ya ce, zai koma birnin don aiki a wata mai zuwa:

Jirgin sama mai lamba CA4111 ya sauka a jiya da karfe 21 da minti 53 a filin saukar jiragen sama na Beijing. Bayan misalin mintoci 20, wani namijin dake da furfura mai sanye kwat da wando masu launin toka-toka da wata matar dake dauke da wani jariri sun fito daga dakin 'yan tafiya cikin kasa. A kan hanyarsa zuwa wurin Taxi, wannan namiji ya gaya wa manema labaru cewa, " ni dan Amurka ne, ina aiki a asusun kudin ba da taimako ga matalauta, na sauka birnin Lhasa a makonni 3da suka wuce don yin aiki. Ina cikin otel a yayin da ake tada tarzomar Lhasa, ban ga faruwar batun ba, kuma ban ga kakkarfan motoci masu dauke da makamai a kan hanya ba, amma daga baya, na ga kantunan da aka kone."

"Yanzu, kura ta lafa a birnin Lhasa, gwamnatin kasar Sin ta aiwatar da ayyuka da dama, gwamnatin ta kula da halin da ake ciki sosai da sosai. ina zama cikin lami lafiya, ban ji tsoro ko kadan ba. Na gamsu da tafiyata a jihar Tibet. A wata mai zuwa, zan je birnin Lhasa don cigaba da aiwatar da aikin taimakawa matalauta."

Namijin ya fada wa manema labaru cewa, waccan mata ita ce matan abokin aikinsa, sun dawo birnin Beijing daga birnin Lhasa tare. Namijin bai fadi sunansa ba, amma a karshe ya yi murmushi tare da cewa, "gwamnatin kasar Sin ta kula da batun Lhasa da kyau a cikin lamarin Tibet."