Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-20 21:21:24    
Ba za a iya hana ci gaban Tibet ba

cri

Kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin ya ruwaito mana labari da cewa, Pagbalha Geleg Namgyai, mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya rubuta bayani da cewa, tabbas ne yunkurin Dalai Lama na neman raba jihar Tibet daga kasar Sin zai ci tura, haka kuma, babu wani irin karfi da zai hana ci gaban bunkasuwar Tibet.

Jaridar 'Tibet Daily' da aka wallafa a ran 20 ga wata ta kaddamar da bayanin da Pagbalha Geleg Namgyai ya rubuta. Pagbalha Geleg Namgyai yana ganin cewa, rukunin Dalai Lama shi ne ya shirya mummunan tashin hankali da tsirarrun masu laifuffuka suka yi a birnin Lhasa. Ainihin burinsa shi ne yunkurin ta da rikici a daidai wannan muhimmin lokaci da ke jawo hankali, da kuma neman tsananta lamarin, har zuwa lamarin zubar da jini, rukunin Dalai Lama ya nemi lalata kwanciyar hankali da jituwa a harkokin siyasa. Da babbar murya Pagbalha Geleg Namgyai ya yi tir da lamarin, ya kuma nuna matukar fushi.(Tasallah)