Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-20 16:57:24    
Canzawar tufaffi ta jama'ar kasar Sin

cri

A lokacin taro a karo na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a zagaye na 11 da aka shirya a kwanan baya a nan birnin Beijing, wakiliyarmu ta kai ziyara ga wasu wakilai musulmi,wadansa suka fito daga manoma, da masu aikin masana'antu, da limaman masallatai, da shehu malamai, da kuma jami'an gwamnatin kasar Sin. Inda suka bayyana canjewar musulmi na kasar Sin a fannin sa tufaffi tun shekaru 30 da suka wuce, ta yadda ake iya ganin sakamakon da ke kawo alheri ga jama'ar kasar Sin da kasar ta samu tun bayan da aka yi gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje.

Mataimakin shugaban majalisar musulunci ta birnin Lanzhou na lardin Gansu Su Guanglin ya waiwayo cewa, "Yau da shekaru 30 da suka wuce, mutane su kan kashe kudin Sin RMB yuan goma kawai don sayen riga da wando, kuma kullum suna sanya su har shekaru uku ko hudu. A da, a kan kashe kudi kadan don sayen wata karamar hula mai launin fari kamar musulmi 'yan kabilar Hui suke sanyawa, kuma ba za a canja sabuwar hula ba, har sai lokacin da hular ta lalace."

'Dan majalisar wakilai Su Guanglin da ke da shekru kusan 70 da haihuwa, ya shaida dukkan yunkurin yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje na kasar Sin. Ya ce, kafin a yi gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje a nan kasar Sin, mutane ko tsoffafi ko yara ko maza ko mata, dukkansu suna sanya tuffafi masu launuka shudi, da fari, da baki, ko kore iri na tuffafin soja na kasar, kuma wadancan tuffafi suna da siga daya. Lallai ga mutane a lokacin, sun sanya tuffafi ne domin kiyaye dumi kawai.

A ganin yawancin mutane, tun daga kasar Sin ta soma yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje a shekarar 1978, sana'ar tuffafi ta kasar ta soma samun bunkasuwa, kuma ra'ayin zamani na Sinnawa ya fara farfadowa. Bisa karfafa yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, da kuma kara samun bunkasuwar tattalin arziki, launuka da sigar tuffafi su ma suna ta kara karuwa. Kan maganar canjewar launukan tuffafi, 'yar majalisar wakilai daga kabilar Uygur ta jihar Xinjiang Halitan, ta ce, "A lokacin da nake karatu a sakandare, wani ya sayo mana wani zane mai ruwan hoda na Dacron (?)daga birnin Shanghai, kuma mamata ta yi amfani da shi don dinka mini wata riga ta Dacron. Mutane da yawa sun yi hassada kan wannan, kuma sun ce, 'rigarki tana da kyau.' Saboda haka, na yi alfarma sosai."

Dacron na da abubuwan musamman kamar su: mai taushi numfashi, da maras kauri, da kuma yi wanke da sauki, da dai sauransu, a sakamakon haka, mutane da yawa suna son dacron a lokacin. Ya zuwa karni na 90, a hakika dai sana'ar tuffafi na kasar Sin ta kai ga ma'aunin kasashen duniya, zane na irin halitta, kamar su: auduga, da silik, da dai sauransu, sun fi samun karbuwa. Bayan haka kuma, a lokacin da ake zana tuffafi a fannonin siga, da launuka, a kan yi la'akari da shekarun haihuwa na jama'a, da kuma sana'a'o'insu.

'Dan majalisar wakilai daga jihar Xinjiang Ashar Turxun, ya waiwayo cewa, "A lokacin da nake karatu a jami'a a karni na 90, zaman rayuwarmu ta samu kyautattuwa sosai. Bisa bunkasuwar tattalin arziki, da sauyawar ra'ayi, ina da wasu tuffafi masu kyau. Wadancan tuffafi kuma suna da siga ta zamani."

'Yar majalisar wakilai Halitan ta gayawa wakiliyarmu cewa, tun daga karni na 90, tuffafin da mutanen jihar Xinjiang suke sanyawa, sun samu canzawa bisa karfafa yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje. Ta ce, "A kasuwar jihar Xinjiang, ana iya sayen tuffafin da suka fi kyan gani da zamani daga manyan birane, kamar su Beijing, da Shanghai, da Guangzhou, har ma daga kasashen waje. Sabo da 'yan kananan kabilu na jihar Xinjiang suna son yin ado, don haka, su kan kashe kudi da yawa kan tuffafi."

Ya zuwa karni na 21, bukatun da Sinnawa ke yi kan tuffafi ba kiyaye dumi kawai ba, suna fatan tuffafinsu za su nuna halinsu na kansu. Kamar 'dan majalisar wakilai na kabilar Hui daga jihar Ningxia Bai Shangcheng ya ce, "Yanzu siga da launuka na tuffafi suna da yawa, kowa da kowa ke iya sayen tuffafin da suke so. Ko shakka babu, sharadi na farko shi ne, tattalin arziki na kasarmu ya samu bunkasuwa, don haka, muna da isasshen kudi don sayen tuffafi."

Canzawar tuffafi ta jama'ar kasar Sin, ita ce wani sakamakon kasar ta samu wajen gudanar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, ita ce kuma ta nuna cewa, zaman rayuwar jama'ar kasar ta kai wani sabon matsayi. Jin Lantying, 'yar majalisar wakilai daga jihar Shandong ta ce, "Na taba zaman 'yar majalisar wakilai na taro a zama na 9 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin. Na kan kwatanta da hotunan da na dauka a lokacin da na yanzu. A da, tuffafin da na sa suna mai da ni bakauya, amma yanzu na yi kamar na fi kuruciya bisa na da."

Lamarin sanya tuffafi da jama'ar kasar Sin ke sawa ya nuna sauyewar dukkan kasar Sin tun shekaru 30 da suka wuce. Kasar Sin ta samun cigaba sosai a sakamakon manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje da kasar ke dauka.