Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-18 16:48:26    
Ya kamata a kiyaye zaman lafiya a zirin Taiwan, da kuma sa kaimi ga bunkasuwar gabobin biyu

cri
A ran 18 ga wata, firaministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao ya bayyana a birnin Beijing cewa, kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Taiwan, da kuma sa kaimi ga bunkasuwar gabobin biyu, ya kamata su zama manyan jigo na dangantakar dake tsakanin gabobin biyu na mashigin tekun Taiwan.

An rufe taron shekara shekara na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a karo na 11 a ran 18 ga wata a birnin Beijing. A gun taron manema labaru da aka shiya bayan taron, Mr. Wen Jiabao ya bayyana cewa, dalilin da ya sa kasar Sin take adawa da "shigar da Taiwan cikin M.D.D ta hanyar kada kuri'ar raba gardama" shi ne idan an cimma burin nan, zai canja halin da muke ciki yanzu, wato Taiwan da babban yankin kasar Sin suna kasa daya ne, tilas ne zai kawo illa ga dangantakar dake tsakanin gabobin biyu, da moriyar jama'ar gabobin biyu, wannan zai sa dangantakar da ke tsakanin gabobi biyu a tsakanin mashigin tekun Taiwan ta tsananta sosai, kuma kawo illa ga zaman lafiya a zirin Taiwan, har ma a yankin Asiya da Pacific.

A sa'I daya kuma, Mr. Wen Jiabao ya jadadda cewa, yana fatan an iya farfado da shawarwarin shimfida zaman lafiya dake tsakanin gabobin biyu tun da wuri bisa sharadin kasar Sin daya tak a duniya, ana iya tattaunawa kan kowane irin batuttuwa, har ma wadansu batuttuwa masu muhimmanci kamar kawo karshen hali na abokan gaba da ake ciki yanzu. (Zubairu)