Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-18 16:33:45    
Firaministan Sin ya gana da manema labaru na gida da na ketare

cri

Wakilin gidan rediyon CRI ya ruwaito mana labari cewar, an rufe zama na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a karo na 11 yau 18 ga wata a nan birnin Beijing. Bayan taron, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya yi wata ganawa tare da manema labaru na gida da na ketare, inda ya amsa tambayoyi game da hanyar da za a bi wajen raya kasa cikin nan shekaru biyar masu zuwa, da sauran batutuwan dake jawo hankali a nan kasar Sin.

Firaminista Wen ya ce, batutuwa hudu da ya fi dora muhimmanci a kansu sun hada da: Na farko, bunkasa tattalin arziki cikin sauri ba tare da tangarda ba. Na biyu shi ne, zurfafa yin gyare-gyare kan tsarin tattalin arziki da na siyasa. Na uku wato sa kaimi ga shimfida turbar adalci a zamantakewar al'umma. Na hudu wato na karshe shi ne, inganta ayyukan wayewar kai irin na gurguzu.

Yayin da yake tabo magana kan burin raya kasar Sin a nan gaba, Mr. Wen ya bayyana cewar, a cikin shekaru biyar masu zuwa, ya kamata a kara habaka tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama'a, da daukaka cigaban zamantakewar al'umma, da kara samun cigaba wajen budewa kasashen waje kofa da yin gyare-gyare. A wannan shekara kuma, kasar Sin za ta sanya kokari wajen hana bunkasuwar tattalin arziki fiye da kima daga dan sauri kadan, da dakatar da hauhawar farashin kaya, tare kuma da raya tattalin arziki cikin sauri ba tare da tangarda ba.

A waje daya, yayin da ya ambaci dangantakar dake kasancewa tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan, firaminista Wen ya sake nanata matsayin da gwamnatin Sin take tsayawa a kai na nuna adawa ga "jefa kuri'ar raba gardama kan shigar Taiwan cikin Majalisar Dinkin Duniya", kuma yana fatan farfado da shawarwari cikin ruwan sanyi tun da wuri tsakanin gabobin biyu a karkashin ka'idar "kasancewar kasar Sin daya tak a duk duniya". Ya kuma yi nuni da cewar, babban yankin kasar Sin zai cigaba da fadada mu'amalar cinikayya tsakaninsa da Taiwan, da daga matsayin hadin-gwiwarsu, ta yadda za a cimma burin yin musanyar jiragen sama, da wasiku, da cinikayya kai tsaye tsakanin gabobin biyu.

Dangane da ringingimu da aka yi kwanan baya a babban birnin Tibet wato Lhasa, Wen Jiabao ya ce, akwai kwararan shaidu wadanda suka tabbatar da cewar, kungiyar Dalai Lama ce ta tayar da wannan tarzoma, a wani yunkurin lalata zaman lafiya a Lhasa. Ya ce, gwamnatin kasar Sin na da karfi sosai wajen kiyaye zaman lafiya da tabbatar da doka da oda a zamantakewar al'umma a Tibet, haka kuma, za ta cigaba da marawa Tibet baya wajen habaka tattalin arzikinta da daukaka cigaban zamantakewar al'umma.

Kazalika kuma, firaminista Wen ya nuna cewar, jama'ar kasar Sin suna sa ran alheri za a gudanar da gasar wasannin Olympics da kyau, kuma suna fatan fadada hadin-gwiwa da dankon aminci tsakanin al'ummomin kasashe daban-daban. A waje daya kuma, Wen Jiabao ya amsa tambayoyin manema labaru dangane da batun yin gyare-gyare kan tsarin siyasa da na tattalin arziki na kasar Sin, da batun sa ido kan zamantakewar al'umma da bada hidima ga jama'a.(Murtala)