Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-18 13:00:30    
Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya bayyana cewa, ya kamata a gaggauta ciyar da raya zaman gurguzu na zamani gaba

cri

A ran 18 ga wata a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya furta cewa, ya kamata a cigaba da raya gina zaman al'umma mai wadata a duk fannoni, da gaggauta ciyar da raya zaman gurguzu na zamani gaba.

Hu Jintao ya yi wannan furuci ne a gun bikin rufe taron shekara-shekara da aka saba yi na sabuwar majalisar jama'ar kasar Sin. Ya ce, aikin gyare-gyare da bunkasuwa na kasar Sin ta shiga cikin wani muhimmin lokaci, domin fuskantar da sabon yanayi da sabon nauyin da ake dora mana, ya kamata a tabbatar da ra'ayin bunkasa kasa ta hanyar kimiya, da cigaba da 'yantar da tunanin jama'ar kasar, da nacewa ga gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, da kuma sa kaimi ga bunkasuwa ta hanyar kimiya don raya zaman al'umma mai jituwa.

A sa'i daya, Hu Jintao ya nuna cewa, duk irin wahalolin da za a fuskanta a kan hanyar gaba, idan a nace ga bin hanyar zaman gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin, a hada gwiwa da yin kokarin aiki bisa hangen nesa, dole ne, a iya cimma sabuwar nasarar gina zaman al'umma mai wadata, a iya tabbatar da farfadowar al'ummar Sin don ba da sabuwar babbar gudummowa ga dan Adam.(Lami)