Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-18 10:17:47    
(Sabunta)An rufe taron shekara shekara na farko na sabuwar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin

cri

A ran 18 ga wata da safe a birnin Beijing, bayan da aka kammala dukkan ajanda, an rufe taro na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 11 cikin nasara.

A gun taron rufewa, Mr Hu Jintao, wanda ya sake cin zaben shugaban kasa, ya bayyana cewa, zai sauke nauyin da ke bisa wuyansa bisa ga kundin mulkin kasa ya dore masa yadda ya kamata, zai yi kokari sosai, domin bauta wa jama'a da kuma kasar Sin, ko kusa ba zai ci amanar babbar fatar wakilai daban daban da jama'a ta kabilu daban daban ba.

A sa'i daya kuma, Mr Hu ya jaddada cewa, ma'aikatan sababbin hukumomin kasar Sin suna da babban nauyin da jama'a ke dore musu, sabo da haka ne, kamata ya yi su amsa kirar zamani, da biya bukatar jama'a, da kuma tsaya kan babbar manufar bauta wa jama'a bisa zuciya daya a yayin da suke aiwatar da ayyukansu, da tabbatar da ikon jama'a da moriyarsu, domin samar wa jama'a alheri. Mr Hu ya ci gaba da cewa, kamata ya yi ma'aikata su yi amfani da ikonsu yadda ya kamata, da kuma yarda da jama'a su sa ido kan su cikin sahihiyar zuciya, kada su ci hanci da rashawa, su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Mr Wu Bangguo ya bayyana a gun taron rufewa cewa, tabbas ne wannan taro zai kara sa kaimi ga jama'ar kabilu daban daban na kasar Sin da su hada kansu sosai, da rubanya kokari, domin samu nasarar kafa wata al'umma mai wadata a fannoni daban daban, da sha'anin gurguzu da ke da abubuwan muamman na kasar Sin.

A gun taron rufewa, wakilan jama'ar kasar Sin da yawansu ya kai kusan dubu 3 sun jefa kuri'a kan shirin kuduri kan rahoton aiki na gwamnati, da shirin kudurin rahoton kasafin kudi, da rahoton aiki daga kotun koli ta kasar Sin, da kuma hukumar koli ta bin bahasi ta jama'ar kasar Sin.(Danladi)