Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-17 20:27:15    
An tsai da sauran 'yan majalisar gudanarwa a gun taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin

cri
A ran 17 ga wata da yamma, a birnin Beijing, an kira cikakken taro na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta karo na 11.

A gun taron, bisa sunayen mutanen da Wen Jiabao, firayim ministan majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya gabatar, an tsai da sauran 'yan majalisar gudanarwa, wato Li Keqiang da Hui Liangyu da Zhang Dejiang da Wang Qishan sun zama mataimakan firayim minsitan kasar, yayin da Liu Yandong da Liang Guanglie da Ma Kai da Meng Jianzhu da kuma Dai Bingguo suka zama membobin majalisar. Ban da wannan kuma taron ya sanar da sunayen babban sakataren majalisar gudanarwa da ministoci daban daban da shugabannin kwamitoci daban daban da shugaban bankin jama'ar kasar Sin da kuma shugaban hukumar binciken kudi ta kasar.

Bisa kudurin da taron ya tsayar, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya ba da umurnin shugaba na biyu don nada majalisar gudanarwa da taron ya zartar ta hanyar jefa kuri'a da kuma membobinta.(Kande Gao)