Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-17 15:12:54    
Kamfanonin watsa labaru na kasashen waje sun mai da hankali kan sababbin shugabannin kasar Sin da aka zaba a tarurrukan majalisu biyu

cri
A kwanakin nan, kamfanonin watsa labaru na kasashen waje sun bayar da labaru cewa, an zabi sababbin sahugabannin kasar Sin a gun taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, kuma sun mai da hankali kan batuttuwa da kalubalen da sababbin shugabannin za su fuskanta.

Manyan kamfanonin watsa labaru na duniya, kamarsu kamfanin dillancin labaru na AP, da na Reuters, da na AFP da dai sauransu sun bayar da labaru da yawa a ran 15 ga wata cewa, ran nan, a gun taron na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a karo na 11, an zabi Mr. Hu Jintao ya ci gaba da zama shugaban jamhuriyar jama'ar kasar Sin, da kuma shugaban kwamitin soja na tsakiya na kasar. Mr. Wu Bangguo ya zama shugaban zaunanen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a karo na 11, Mr. Xi Jinping kuma ya zama mataimakin shugaban jamhuriyar jama'ar kasar Sin.

Kamfanin dilancin watsa labaru na AP ya ba da labari cewa, a karkashin jagorancin shugaba Hu Jintao da sauran shugabanni, tattalin arzikin kasar Sin yana ta ci gaba da bunkasuwa cikin sauri a shekarun nan, sifar kasar Sin kuna tana ta ci gaba da inganta. A cikin labarin, an ce, sababbin shugabannin kasar Sin suna faskatar kalubale mai tsanani sosai, kamarsu harkokin zirga-zirga, da samar da wutar lantarki, da shirin da aka tsara don gudanar da harkokin gwamnati, da dai sauransu.

Sauran kamfanonin watsa labaru kamarsu Itar-tass News Agency, da Jiji News Agency, da EFE suma sun bayar da labaru game da zabin sababin shugabannin kasar Sin.

A ran 14 ga wata, kamfanonin watsa labaru na kasashen waje sun mai da hankali kan rufe taron na farko na majalisar ba da shawara a karo na 11, sun bayar da labarin cewa Mr. Jai Qinglin ya ci gaba da zama shugaban majalisar ba da shawara na kasar Sin, a sa'I daya kuma, sun yi bayani kan aikin majalisar ba da shawara na kasar Sin da kuma ajandar taron. (Zubairu)