
Bisa sakamakon kuri'un da aka jefa a gun cikakken taro na majalisa ta 11 ta wakilan jama'ar kasar Sin, an ce, Wen Jiabao ya zama firayim minista na majalisar gudanarwa ta Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin.

Mr.Wen Jiabao
A ran 16 ga wata, an kira cikakken taro na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta karo na 11 domin tabbatar da firayim ministan majalisar gudanarwa da mataimakin shugaban kwamitin aikin soja na tsakiya na kasar da membobinsa, da kuma zaben shugaban kotun koli ta jama'ar kasar Sin da kuma babban mai gabatar da kara na hukumar koli ta gabatar da kararraki ta kasar.
Kuma bisa sakamakon kuri'un da aka jefa a gun taron, an ce, Guo Boxiong da Xu Caihou sun zama mataimakan shugaban kwamitin aikin soja na tsakiya na kasar Sin. Wang Shengjun ya zama shugaban kotun koli na jama'ar kasar Sin, yayin da Cao Jianming ya zama babban mai gabatar da kara na hukumar koli ta gabatar da kararraki ta kasar.(Kande Gao)
|