Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-15 17:16:37    
Jaridar People's daily ta taya murnar rufe taron CPPCC da aka yi tare da nasarori

cri
Yau jaridar people's daily ya bayar da wani bayanin edita, don taya murnar rufe taro na farko na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta 11, ko CPPCC a takaice, da aka yi cikin nasara.

Bayanin ya ce, taron ya bi manyan jigogi guda biyu, wato hadin kai da dimokuradiyya, wadanda suka bayyana kuzari na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin da kuma irin wannan hanyar dimokuradiyya da ake bi, wanda ba shakka zai taka muhimmiyar rawa wajen kara sa kaimi ga yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, haka kuma zai taimaka wajen kara bunkasa kimiyya da raya siyasar dimokuradiyya ta gurguzu.

Sharhin ya ce, nacewa ga bin hanyar cigaban siyasa ta gurguzu da ke da halin musamman na kasar Sin na bukatar majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta kara taka muhimmiyar rawa, sa'an nan a yi kokarin yin shawarwari a fannin siyasa, kuma a kyautata tsarin sa ido na dimokuradiyya, a kara inganta tsarin sa hannu cikin harkokin siyasa, don a samar da tabbaci a fannin siyasa ga bunkasuwar jam'iyyar kwaminis ta Sin da kuma bunkasuwar kasar Sin.(Lubabatu)