Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-15 16:30:25    
Akwai kwararan hujjojin da suka shaida cewa gungun mabiya Dalai ne ya kulla makarkashiyar yin harkar shuka barna a Lhasa na Tibet

cri

Jiya Jumma'a, wani jami'in jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin ya furta cewa, akwai kwararan hujjojin da suka shaida cewa, harkar shuka barna da wasu tsirarrun mutane suka tayar kwanan baya ba da dadewa ba a Lhasa na Tibet ya samu sa hannun gungun mabiya shugaban addinin Buddah Dalai Lama mai gudun hijira. Jama'a 'yan kabilu daban-daban na Tibet sun kadu kuma na fusata kwarai da gaske dangane da irin wannan danyen aikin da aka barkata.

Sa'annan jami'in ya kara da cewa, kwanan baya dai, wassu tsirarrun mutane sun yi rikici mafi muni na yin duke-duke da kwashe-kwashe da kuma na kone-kone da zummar haifar da tsaiko ga odar zamantakewar al'ummar jihar Tibet da kuma yin barazana ga lafiyar rayuka da dukiyoyin jama'a. Sassan da abin ya shafa na Tibet suna nan suna daukar tsattsauran matakai bisa doka na shawo kan lamarin.

A lokaci guda, jami'in ya yi nuni da cewa, kasar Sin na da karfi sosai wajen kiyaye zaman karko na jihar Tibet da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama'a 'yan kabilu daban-daban na jihar. Labuddah hakar wadannan tsirarrun mutane ba za ta cimma ruwa ba! ( Sani Wang)