Ran 14 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Zhang Mingqi mataimakin shugaban kungiyar 'yan kwadago na dukkan sassen kasar Sin ya ce, kungiyar za ta yi kokarin kafa dokar yarjejeniyar yin kwangilar aiki domin ba da taimako wajen aiwatar da wannan doka.
Mr. Zhang Mingqi ya ce, dukkan kamfannonin da ke cikin yankin kasar Sin, masana'antun da ke cikin hannun gwamnati, da masu zaman kansu, da na kasashen waje, dole ne su bi dokar yarjejeniyar yin kwangilar aiki. Kungiyar 'yan kwadago za ta yi kokarin sa kaimi ga hukumomin da abin ya shafa da su kafa sharudda da dokoki na wannan doka, ta haka domin tabbatar da ganin ana tafiyar da wannan doka yadda ya kamata.

Mr. Zhang Mingqi ya jaddada cewa, ya kamata kamfannoni su dukufa ka'in da na'in wajen bin wannan doka. Tilas ne kada su bata moriyar 'yan kwadago domin nema riba.
|