Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-14 10:27:14    
Sabunta: An rufe taron shekara shekara na zama na farko na sabuwar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa

cri

Ran 14 ga wata da safe a nan birnin Beijing, an rufe zama na farko na kwamitin dukkan sassen kasa na karo na 11 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin, shugabanni Hu Jintao, da Wu Bangguo, da Wen Jiabao sun halarci wannan taro.

Mr. Jia Qinglin wanda ya sake zama shugaban majalisar ya jagoranci bikin rufe taron. Ya ce, shekarar da muke ciki ita ce shekara ta farko ta aikin sabuwar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, ya kamata sabuwar majalisar ta lura da sabon canje-canje na halin da ake ciki, da biyan bukatun jama'a, da yin amfani da tsarinta na musamman da matsayin rinjaye, ta haka domin aiwatar da ayyukanta yadda ya kamata, wato ba da shawara kan harkokin siyasa, da sa ido ta hanyar dimokuradiyya, da kuma yin aikin gwamnati. Haka kuma za su iya ba da sabuwar gudummawa wajen gina zaman al'umma mai wadata, da bunkasa gurguzu da ke bayyana halin musamman na kasar Sin. Ya jaddada cewa, dole ne majalisar ta mai da aikin sa kaimi ga bunkasuwa ya zama aiki mafi muhimmanci, da kuma lura da manyan batutuwa biyu na hadin kai da dimokuradiyya, da kuma kara yin nazari da ayyuka domin inganta karfin aiwatar da ayyukanta.

A gun taron da aka yi, an kada kuri'a kuma an zartar da rahoto kan aikin zaunanen kwamitin majalisar ba da shawara da aka gabata, da rahoton game da duddubawar shirin gabatar ra'ayoyi da kuma kudurin siyasa na wannan taro.