Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-14 10:09:36    
An rufe taron shekara-shekara na zama na farko na sabuwar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin

cri

Ran 14 ga wata da safe, a nan birnin Beijing, an yi bikin rufe taro na zama na farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na karo na 11 na jama'ar kasar Sin. Shugabannin kasar Sin kuma shugabannin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Hu Jintao da Wu Bangguo da Wen Jiabao sun halarci bikin rufe taron.


Mr. Jia Qinglin wanda aka zabe shi shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar ya shugabanci bikin rufe taron. A gun taron, an zartas da rahoton aiki na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar da rahoton duddubawar shirin shawarar da aka gabatar a gun taron da kudurin siyasa na taron.


A kan zaben majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ko wace shekaru biyar-biyar, taron da aka yi na wannan gami shi ne karo na farko bayan da aka zabi sabuwar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasata kasar. A gun taron da aka yi na kwanakin 11, mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar da yawansu ya kai fiye da 2000 da suka zo daga  kungiyoyin jam'iyyu da dama da kuma kabilu da da fannoni daban daban sun ba da shawararsu kan manyan batutuwan da aka fi jawo hankulan mutane da batutuwan da ke shafar babbar ka'ida Sin a gun taron, kuma an zabi shugaban harkokin siyasa na kasar da sabuwar hukumar harkokin siyasa na kasar.(Bako)