Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-13 21:40:12    
Mr Jia Qinglin ya sake zama shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin

cri

A ran 13 ga wata a babban zauren taruwar jama'a da ke birnin Beijing, an shirya cikakken zama na 4 na taron farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta 11. Taron ya zabi zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin Mr Jia Qinglin ya zama shugaban majalisar, a sa'i daya kuma, an zabi mataimakan shugaban majalisar da yawansu ya kai 25. Ban da wannan kuma, an zabi zaunannun mambobi 298.

Bisa dokar zabe ta taron farko na majalisar ta 11, an ce, an jefa kuri'a ne ba tare da sanya suna ba, kuma an zabi shugaba, da mataimakan shugaba, da babban sakatare, da kuma zaunannun mambobbi ne bisa tsarin 'yan takara sun fi guraben takara yawa. 'yan takara wadanda suka samu yawan kuri'u da ya fi rabi sun kama karagar mulkinsu.(Danladi)