Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-13 15:11:33    
Maliya Mati, wata 'yar majalisar wakilai ta kasar Sin daga flanton Pamirs

cri
Yanzu kasar Sin na gudanar da tarurrukan majalisu biyu a nan birnin Beijing. A cikin wadanda ke halartar tarurrukan biyu, akwai wata 'yar majalisar wakilai ta musamman, sunanta Maliya Mati. A cikin 'yan majalisar wakilai ta kasar Sin a karo na 11 da yawansu ya kai 2987, garin Maliya Mati ya fi da nisa bisa birnin Beijing, babban birnin kasar. Maliya Mati ta fito ne daga gundumar Kezilesu mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta jihar Xinjiang, ita ce kuma 'yar majalisar wakilai daga kabilar Kirgiz daya tak a nan kasar Sin.

Kabilar Kirgiz tana daya daga cikin kananan kabilu guda goma masu bin addinin Musulunci na kasar Sin, yawancinsu suna zama a flanton Pamirs, yawan 'yan kabilar ya kai sama da dubu 160. Bisa dokar zabe da abin ya shafa ta kasar Sin, ana iya zabi 'dan majalisar wakilai ko 'yar majalisar wakilai daya daga kabilar Kirgiz. Abin farin ciki shi ne Maliya Mati ta zama wannan 'yar majalisar wakilai daya tak. To, masu sauraro, yanzu bari mu kusata wannan madam daga kabilar Kirgiz.

Bayan da ta gama abincinta na safe, sai Maliya Mati ta bude kamputa, don kara abubuwan da ke cikin jawabin da za ta yi a gun taron kananan kungiyoyi da za a shirya a wannan rana da safe.

A shekarar 2003, Maliya Mati da ke da shekaru 32 da haihuwa a lokacin can ta zama wata 'yar majalisar wakilai ta taro a karo na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a zagaye na 10. A lokacin can kuma ita ce wata jami'a ta yau da kullum da ke aiki a kananan hukumomi a kauyuka na gundumar Kirgiz mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta jihar Xinjiang.

Wakilinmu ya samu wannan daukan sauti ne a lokacin da Maliya Mati ke yin jawabi a gun taron kungiyar wakilai ta jihar Xinjiang game da taro a karo na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a zagaye na 10 da aka shirya a shekaru biyu da suka wuce.

Ranar 8 ga watan Maris na shekarar 2006, rana ce ta bikin mata na duniya. A wannan rana kuma, akwai wani abin farin ciki ga Maliya Mati da ke halartar taro na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a zagaye na 10, wato firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya halarci taron kungyiyar wakilai ta jihar Xinjiang, don sauraren ra'ayoyi. Bayan da wakilai fiye da goma suka yi jawabi, Mr. Wen Jiabao ya ba da wata shawara, wato bayar da damar yin jawabi ta karshe ga wani wakili ko wakiliya daga kananan hukumomi. Bayan da ya ga sunan Maliya Mati da ta fito daga kauye a takardar sunaye, ya ce, "Bari mu ji ra'ayi na Maliya Mati." Maliya Mati ta tuna da cewa, "A lokacin, na gabatar da wata shawara ga firayin minista Wen Jiabao, wato ko kasarmu ke iya gudanar da harkokin ba da tabbaci ga ma'aunin zaman rayuwa mafi kankanta a kauyuka kamar ake yi a birane? Mr. Wen Jiabao ya karbi shawarar da na yi, kuma ya shigar da ita cikin rahoton ayyuka na gwamnati a shekara mai zuwa, inda ya rubuta cewa, za a kafa tsarin tabbatar da matsayin zaman rayuwa mafi kankanta na kauyuka a duk kasar Sin."

Garin Maliya Mati kuma ya kasance ne a wuri na farko da kasar Sin ke gudanar da tsarin tabbatar da matsayin zaman rayuwa mafi kankanta na kauyuka. Yanzu, ana gudanar da tsarin a yankunan da ke yamma maso tsakiyar kasar Sin a dukkan fannoni. A nan gaba ba da dadewa ba, za a kafa tsarin a duk kasar Sin.

Tun daga shekarar 2003 har zuwa shekarar 2007, yawan shawarwari da Maliya Mati ta gabatar a gun babban taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ya kai sama da 50, hukumomin gwamnati da abin ya shafa sun yi bincike da nazari sosai kan wadannan shawarwari, har ma sun ba da amsa kan su. Saboda tana da kwarewa a shekaru biyar da take zaman 'yar majalisar wakilai a gun taro a karo na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a zagaye na 10, don haka, an sake zabenta zama 'yar majalisar wakilai ta wannan taro a zagaye na 11.

A gun taron, a matsayinta na wata jami'a daga kananan kabilu, ta ba da shawara ga gwamnatin kasar Sin da ta kara mayar da hankali kan horar da jami'an kananan kabilu, musamman ma jami'ai mata. "A garinmu, jami'an kananan kabilu, musamman ma jami'ai mata kamar ni ba su da yawa. Ina fatan kasarmu za ta kara horar da jami'an kananan kabilu masu ilmin kimiyya da fasaha da kuma al'adu, ta yadda za su iya jagorar da manoma da makiyaya da su neman zaman rayuwa mai dadi ta hanayyensu."

A lokacin kusan karewar ziyara, Mliya Mati ta gayawa manema labaru cewa, a shekaru biyar masu zuwa, za ta kara yin iyakacin kokarinta, da kuma sauke nauyin da ke bisa wuyanta na wata 'yar majalisar wakilai, don ba da taimakonta kan bunkasuwar kasa da al'umma.

"Na yi alfahari a lokacin da nake nuna wahaloli da matsalolin da farar hula ke gamuwa da su a zaman rayuwarsu na yau da kullum ga manyan shugabannin kasarmu, da kuma jawo hankulansu sosai, har sa kaimi ga warware matsalolin, ta yadda zan iya taimakawa mutanen garinmu don kawar da talauci."