Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-12 17:46:31    
Kasar Sin soma sabuwar kwaskwarima kan hukumomin gwamnatinta

cri
A gun taron majalisar dokokin kasar Sin da aka yi a ran 11 ga wata, majalisar gudanarwa ta kasar Sin, wato gwamnatin kasar ta gabatar wa taron da wani shirin yin kwaskwarima kan hukumominta domin soma yin sabuwar kwaskwarima kan hukumominta a karo na 6 tun daga shekarar 1982. Manazarta sun ce, wannan kwaskwarima za ta sa kasar Sin ta ci gaba wajen cimma burin kafa wata gwamnati mai ba da hidima.

A gun taron, Mr. Hua Jianmin, mamba kuma babban sakataren majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya yi wa wakilan jama'a bayani kan wannan shiri. Mr. Hua ya ce, "babban burin da ake son cimmawa domin yin kwaskwarima kan hukumomin majalisar gudanarwa ta kasar Sin shi ne, canja nauyin da ke bisa wuyan gwamnati da daidaita hakki na kowace hukumar gwamnati domin kafuwar hukumomin gwamnati mafi girma. A waje daya kuma, daidaita hakki na hukumomin da suke sa ido kan ayyuka iri iri daga dukkan fannoni da kara karfin hukumar kula da makamashi da kiyaye muhalli da kyautata tsarin masana'antu da zamanintar da yanar gizo da tsarin zirga-zirga da sufuri. Sabo da haka, za a iya cimma burin kara karfin hukumomin da ke kula da harkokin zaman al'umma da ba da hidima ga jama'a bisa kokarin kyautata zaman rayuwar jama'a."

Bisa wannan shirin yin kwaskwarima kan hukumomin gwamnatin kasar, za a kafa sabbin ma'aikatan gwamnati biyar, da suka hada da ma'aikatar masana'antu da zamanintar da yanar gizo da ma'aikatar zirga-zirga da sufuri da ma'aikatar albarkatun kwadago da ba da tabbaci ga jama'a da ma'aikatar kiyaye muhalli da ma'aikatar gidaje da raya kauyuka da birane. A waje daya kuma, za a kafa wata hukumar koli ta tattaunawa da daidaita harkokin makamashi, wato kwamitin makamashi na kasar a cikin majalisar gudanarwa. Kuma za a kafa hukumar makamashi ta kasar Sin. Bayan da aka yi kwaskwarima kan hukumomin gwamnatin kasar Sin, gwamnatin kasar Sin za ta kunshi ma'aikatai 27.

Mr. Wang Yukai, shehun malamin kwalejin harkokin yau da kullum ta kasar Sin ya bayyana cewa, "Irin wannan gyare-gyaren da ake yi zai yi tasiri mai kyau wajen kyautata aikin gwamnati, kuma yana da muhimmanci sosai wajen raguwar kudin da hukumomin gwamnati suka kashewa."

Mr. Chi Fulin, shugaban cibiyar yin nazari kan harkokin gyare-gyare da neman bunkasuwa ta kasar Sin yana ganin cewa, lokacin da ake tsara wannan shirin yin kwaskwarima kan hukumomin gwamnati, an fi jaddada nauyin ba da hidima da ke bisa wuyan gwamnati. Mr. Chi ya ce, "Wannan gyare-gyare za su amfana wa kokarin ba da hidima ga jama'a domin cimma burin kyautata zaman rayuwar jama'a. Kuma zai iya jaddada muhimmin matsayin da gwamnati take ciki wajen ba da hidima ga jama'a."

A cikin dimbin shekarun da suka gabata, a kullum ne gwamnatin kasar Sin tana kokarin tabbatar da mukaminta daidai wajen tafiyar da harkokin mulkin kasar.

Lokacin da yake bayani kan shirin yin kwaskwarima kan hukumomin gwamnatin kasar Sin, Mr. Hua Jianmin ya fi jaddada daidaituwar nauyin da ke bisa wuyan ma'aikatun da suke sa ido kan harkoki daga dukkan fannoni kamar yadda ya kamata.

Lokacin da wakilinmu yake neman labaru daga cikin wakilan jama'a mahalartar wannan babban taro, ya gane cewa yawancin wakilan jama'a suna goyon bayan wannan shirin yin kwaskwarima kan hukumomin gwamnatin kasar Sin.