Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-12 15:51:05    
Kafofin yada labarai na ketare na maida hankulansu kan gyare-gyaren hukumomin gwamnatin Sin

cri
A cikin 'yan kwanakin nan, kafofin yada labarai na ketare sun darajanta zurfafa ayyukan yiwa hukumomin gwamnati gyare-gyare da kasar Sin za ta yi, suna ganin cewar, yin gyare-gyare ba ma kawai yana taimakawa wajen shawo kan kalubale daga fannoni daban-daban na tattalin arziki da zamantakewar al'umma ba, har ma zai iya haifar da kyakkyawan tasiri ga duk duniya.

Bugu da kari, manyan kafofin yada labarai na Amurka sun bayar da labarai da yawa dangane da zurfafa ayyukan yiwa hukumomin gwamnatin gyare-gyare da kasar Sin za ta yi, a ganinsu kuma, gyare-gyaren za su bada cikakken tabbaci ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma a kasar Sin, ko shakka babu, kasashen duniya za su dauke su a matsayin wani abin misali domin bincikensu.

Kwanan baya, jarida mafi kasaita ta Australiya wato Jaridar The Australian ta bayar da labari cewar, kasancewar tsarin manyan hukumomi a nan kasar Sin za ta taimaka wajen daidaita albarkatu, da inganta tafiyar da harkoki yadda ya kamata, haka kuma, ta zama wani sabon cigaba da kasar Sin ta samu wajen cimma burin zamanintar da kasa.

Dadin dadawa kuma, muhimman kafofin yada labarai na Jamus suna sa ido sosai kan batun yiwa hukumomin majalisar gudanarwa ta kasar Sin gyare-gyare. Jaridar Die Welt ta kasar ta ce, gaggan shugabannin kasar Sin sun yi shirin daidaita da takaita hukumomin majalisar gudanarwa ta kasar, ta yadda wadannan hukumomi za su bada jagora ga bunkasuwar tattalin arziki irin na kasuwanni, da zamantakewar al'umma, da harkokin kiyaye muhalli tare cikin jituwa.(Murtala)