Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-12 12:13:14    
Yan Jiechi ya bayyana ra'ayin kasar Sin a kan harkokin diplomasiyya

cri

A ran 12 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya bayyana cewa, samun bunkasuwa cikin lumana da kara yin cudanya da samun nasara tare da moriyar juna da kuma hadin gwiwa don samun jituwa sabbin ra'ayoyi ne na kasar Sin a kan harkokin diplomasiyya a cikin sabon zamani.

A gun taron manema labarai na gida da na waje da aka shirya a ranar a gun taron farko na majalisa ta 11 ta wakilan jama'ar kasar Sin, Mr. Yang ya bayyana cewa, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka kan bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana. Haka kuma kamata ya yi kasashe daban daban ko wadanda suka ci gaba ko da masu tasowa su bi hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, da kuma warware matsalolin da ke tsakaninsu ta hanyar lumana, ta yadda za a iya yin zama tare cikin jituwa da kum samun bunkasuwa tare.

Haka kuma Mr. Yang ya nuna cewa, kasar Sin tana son sada zumunci tare da sauran kasashen duniya da kuma yin cudanya tsakaninta da su domin neman samun hadin kansu.

Ban da wannan kuma Mr. Yang ya ce, ba kawai a kan samu nasara tare don moriyar juna a fannin tattalin arziki da cinikayya ba, har ma a sauran fannoni, kamar siyasa da tsaron kai da al'adu da ilmi. Ya kamata a nemi samun nasara don moriyar juna a tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a iya kafa tushe mai karfi ga dangantakar da ke tsakaninsu, da kuma inganta karfinsu.

Game da hadin gwiwa don samun jituwa, Mr. Yang ya yi bayanin cewa, kasar Sin tana son hadin gwiwa tare da kasa da kasa wajen yin namijin kokari kan raya duniya mai jituwa da kuma samun wata kyakkyawar duniya.(Kande Gao)