Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-11 17:00:15    
Kasar Sin tana da imanin cimma burin raguwar abubuwa masu gurbata muhalli da ake fitarwa

cri

A ran 11 ga wata, Mr. Zhang Lijun, mataimakin ministan babbar hukumar tabbatar da ingancin muhalli ta kasar Sin ya bayyana a nan birnin Beijing, cewar kasar Sin tana da imanin cimma burin raguwar abubuwa masu gurbata muhalli da ake fitarwa da kashi 10 cikin kashi dari a shekarar 2010.

A gun wani taron manema labaru da aka shirya domin farkon zama na babban taron wakilan jama'ar kasar Sin a karo na 11, Mr. Zhang Lijun ya ce, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai wajen raguwar fitar da abubuwa masu gurbata muhalli. A shekarar 2006, babbar hukumar tabbatar da ingancin muhalli ta kasar da gwamnatocin larduna da manyan birane da na jihohi masu cin gashin kansu da kamfanonin samar da wutar lantarki 5 daya bayan daya ne suka kulla yarjejeniyar rage yaduwar abubuwa masu gurbata muhalli. A waje daya kuma, majalisar gudanarwa ta kasar Sin, wato gwamnatin kasar ta bayar da matakan tsimin makamai da raguwar yaduwar abubuwa masu gurbata muhalli da dabarar sa ido kan yadda ake tsimin makamashi da raguwar yaduwar abubuwa masu gurbata muhalli.

Bugu da kari kuma, Mr. Zhang ya ce, gwamnatocin mataki daban-daban na kasar Sin suna kuma mai da hankulansu sosai kan ayyukan tsimin makamashi da raguwar yaduwar abubuwa masu gurbata muhalli. Sabo da haka, za a iya cimma burin raguwar yaduwar abubuwa masu gurbata muhalli da kashi 10 cikin dari ya zuwa shekarar 2010. (Sanusi Chen)