Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-11 16:58:29    
Kasar Sin za ta dauki matakai domin tabbatar da ayyukan maganin abubuwa masu gurbata muhalli sun taka rawa

cri
A ran 11 ga wata, Mr. Zhang Lijun, mataimakin ministan babbar hukumar tabbatar da ingancin muhalli ta kasar Sin ya bayyana a nan birnin Beijing, cewar kasar Sin za ta dauki matakai domin tabbatar da ayyukan maganin abubuwa masu gurbata muhalli suna taka rawarsu kamar yadda ya kamata.

Mr. Zhang ya ce, a cikin 'yan shekarun nan da suka gabata, yankuna daban-daban na kasar Sin sun soma yin amfani da wasu ayyukan maganin abubuwa masu gurbata muhalli. Ko za a iya tafiyar da wadannan ayyuka kamar yadda ya kamata, yana da matukar muhimmanci ga aikin raguwar abubuwa masu gurbata muhalli da ake fitarwa da kokarin kyautata ingancin muhalli.

Ya kuma bayyana cewa, a nan gaba, kasar Sin za ta kara sa ido kan wuraren da ke fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da ayyukan maganin abubuwa masu gurbata muhalli. A waje daya kuma, za ta kara yin bincike da yanke hukunci kan masana'antun da ke fitar da abubuwa masu gurbata bisa doka cikin lokaci. (Sanusi Chen)