Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-11 16:56:39    
kasar Sin ta cimma tudun dafawa sosai wajen yin tsimin makamashi da rage yawan abubuwa masu gurbata muhalli

cri
Ran 11 ga wata, mataimakin direkta na kwamitin yin gyare-gyare da raya kasa ta kasar Sin Xie Zhenhua ya bayyana cewa, a cikin shekarar 2007 kasar Sin ta sanya karfi sosai wajen aikin yin tsimin makamashi da rage yawan abubuwa masu gurbata muhalli, kuma ta cimma tudun dafawa sosai wajen aikin yin tsimin albarkatun kasa da rage yawan abubuwa masu gurbata muhalli.

A gun taron manema labaru na majalisar wakilan jama'a ta cikakken zama na 1 ta karo na 11 da aka yi a wannan ranar, yayin da Xie Zhenhua yake amsa tambayoyin da manema labaru suka yi masa, ya bayyana cewa, a shekarar bara, kasar Sin ta yi shirin gudanar da ayyukan tsimin makamashi da rage abubuwa masu gurbata muhalli daga dukkan fannoni, kuma an kafa tsarin kidayar yawan abubuwa masu gurbata muhalli da kuma kimanta su da kuma tsaida ma'auninsa da tantance su domin yin tsimin makamashi da rage yawan abubuwa masu gurbata muhalli, a hannu daya kuma, an haramta bunkasuwar sana'o'in da ke bata makamashi fiye da kima da kuma fitar da yawan abubuwa masu gurbata muhalli fiye da kima, a dayan kuma an gaggauta yin watsi da sana'o'in da suka samu koma baya wajen yin aikin kawo albarka.

Dadin dadawa kuma, a shekarar bara, kasar Sin ta gaggauta bunkasuwar muhimman ayyuka 10 na yin tsimin makamashi, kuma ta ingiza aikin rage bata makamashi a cikin dubban masana'antu, kuma an cimma manufar kudi da haraji wajen tsimin makamashi da rage abubuwa masu gurbata muhalli, haka kuma an bullo da dokar yin tsimin makamashi da kuma gaggauta karfin wajen aikin dudduba shi.

Bisa kididdigar da aka bayar, a shekarar 2007 yawan GDP da aka samu ta hanyar amfani da makamashi ya rage da kashi 3.27 cikin kashi dari. Yawan iskar So2 da sinadarin iskar Oxygen da ake bukata sun ragu tare.

Xie Zhenhua ya bayyana cewa, a cikin shekarar 2008, kasar Sin za ta dauki kwararrun matakai don ingiza aikin yin tsimin makamashi da rage yawan abubuwa masu gurbata muhalli.(Bako)