Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-11 15:59:05    
An kaddamar da yin gyare-gyare kan majalisar gudanarwa ta kasar Sin

cri
An kaddamar da yin gyare-gyare kan majalisar gudanarwa ta kasar Sin a karo na 6 tun bayan shekarar 1982. Bisa shirin da aka bayar dangane da yin gyare-gyare kan majalisar gudanarwa ta kasar Sin a ran 11 ga wata, an ce, majalisar gudanarwa ta kasar Sin za ta kafa ma'aikatar masana'antu da aikin sadarwa da ma'aikatar sufuri da zirga-zirga da ma'aikatar albarkatun kwadago da jin dadin jama'a da ma'aikatar kiyaye muhalli da kuma ma'aikatar gidaje da raya birane da kauyuka.

Ran 11 ga wata da yamma, an yi cikakken zama na taro na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta karo na 11, inda aka saurari bayanin da aka yi kan shirin yin gyare-gyare kan majalisar gudanarwa ta kasar. Za a yi kwaskwairma kan hukumomi 15, a yayin da ake rage wasu guda 4 a matsayin minista.

Bisa abubuwan da ke cikin wannan shiri, an ce, baya ga sabbin ma'aikatu 5, majalisar gudanarwa ta kasar Sin za ta kafa hukumar tattaunawa a tsakanin manyan jami'an kasar, wato kwamitin makamashi na kasar Sin da kuma hukumar makamashi ta kasar, da ke karkashin shugabancin kwamitin yin gyare-gyare da raya kasar. Kazalika kuma, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar za ta jagoranci hukumar sa ido da kula da abinci da magunguna ta kasar, za ta kuma sauke nauyin da ke wuyanta na sa idon kan ingancin abinci da tono manyan hadarurrukan da ke shafar ingancin abinci.

Cikakken zama na 2 na babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a karo na 17 ya jaddada cewa, za a kafa cikakken tsarin gurguzu na gudanar da harkokin gwamnati a shekarar 2020. Kwararru suna ganin cewa, majalisar gudanawar ta kasar Sin ta kaddamar da yin gyare-gyare a wannan karo ne bisa tushen da ta samu a da, za ta kuma gudanar da ayyukan kwaskwarima cikin himma ba tare da tangarda ba.(Tasallah)