Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-11 15:38:35    
Kasar Sin tana daukar matakai domin rage fitar da iskar dumamar yanayi

cri
Ran 11 ga wata, a nan Beijing, Xie Zhenhua, mataimakin darektan kwamitin yin gyare-gyare da raya kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin tana daukar matakai domin rage fitar da iska mai dumama yanayi.

A wannan rana, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a karo na 11 ta shirya taron manema labaru kan zamanta na karo na farko. A lokacin da yake amsa tambayoyin da manema labaru suka yi masa a gun taron, Xie ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta dauki matakai da yawa domin rage fitar da iskar dumamar yanayi. Tun daga shekarar 1990 har zuwa ta 2005, kasar Sin ta rage yin amfani da makamashi misalin kashi 46 cikin kashi dari wajen samun jimlar GDP, wato ke nan ta rage fitar da iskar carbon dioxide misalin ton biliyan 1.8. Sa'an nan kuma, kasar Sin ta bunkasa makamashin da aka iya sake yin amfani da shi, kamar su iska da hasken rana domin rage dogara da kwal da man fetur. Ban da wannan kuma, kasar Sin ta rubanya kokari wajen dasa itatuwa. A shekaru 25 da suka wuce, itatuwan da aka dasa a kasar Sin sun iya tinkarar iskar carbon dioxide misalin ton miliyan 5.1.

Wannan jami'in Sin ya ci gaba da cewa, nan gaba kasar Sin za ta kara daukar matakai cikin himma wajen raya masana'antu da birane domin neman kara rage fitar da iska mai dumama yanayi tare da raya tattalin arziki.(Tasallah)