Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-10 20:38:08    
Bala'in dusar kankara ba zai iya kawo babbar illa ga aikin shuka hatsi na kasar Sin ba

cri

A ran 10 ga wata a birnin Beijing, mataimakin ministan aikin gona kasar Sin Mr Wei Chao'an ya bayyana cewa, bala'in dusar kankara da ruwan sama da ya faru a wasu wuraren kasar Sin ba zai iya kawo babbar illa ga aikin shuka hatsi na kasar Sin ba a shekarar bana, amma zai ba da tasiri kadan ga kudin shiga da manoma suke samu.

A yayin da yake ganawa da manema labaru a wajen taron farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 11, Mr Wei Chao'an ya bayyana cewa, wannan bala'i ya fi kawo babbar illa ga kayan lambu da 'ya 'yan itatuwa, amma bai kawo illa ga alkama da aka suka a lokacin sanyi ba. Sabo da hukumomin gwamnatin kasar Sin sun yanke shawara kan yanayin bala'in yadda ya kamata, kuma sun dauki matakai masu amfani, a sakamakon haka, samar da kayayyakin gona da kuma farashinsu sun zauna gindinsu bisa gwargwado.

Mr Wei ya ci gaba da cewa, gwamnatoci daban daban za su kara daukar matakai wajen sake ginawa da shuka hatsi a lokacin bazara, da shawo kan cututtukan dabbobi, domin tabbatar da kudin shiga da manoma suke samu.(Danladi)