Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-10 20:25:19    
Kasar Sin ta samu karin hatsi a cikin shekaru 4 a jere da suka wuce

cri

A ran 10 ga wata a birnin Beijing, mataimakin ministan aikin gona na kasar Sin Mr Wei Chao'an ya bayyana cewa, a cikin shekarar bara, yawan hatsin da kasar Sin ta samu ya kai kilo biliayn 500, ta haka, a karo na farko, kasar Sin ta samu karin hatsi a cikin shekaru 4 a jere tun bayan shekarar 1985.

A yayin da yake ganawa da manema labaru a gun taron farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 11, Mr Wei Chao'an ya bayyana cewa, a shekarar bara, kasar Sin ta ci gaba da gudanar da manufofin nuna goyon baya ga manoma, wannan ya sa kaimi ga manoma sosai domin su shuka hatsi, an samu kyakkyawan sakamako. Ban da wannan kuma, Mr Wei ya ci gaba da cewa, a cikin shekarar da ta wuce, matsakaicin kudin shiga da kowane manomi ya samu ya wuce kudin Sin Yuan dubu 4 da dari guda, wanda ya karu da kashi 9.5 daga cikin dari.(Danladi)