Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-10 15:55:31    
Kotunan kasar Sin a matakai daban daban sun dasa aya ga yanke hukunci kan batutuwa fiye da dubu 70 da ke da nasaba da ikon mallakar ilmi

cri
Ran 10 ga wata, a nan Beijing, Xiao Yang, shubagan kotun koli ta kasar Sin ya bayyana cewa, a cikin shekaru 5 da suka wuce, kotunan kasar Sin a matakai daban daban sun dasa aya ga yanke hukunci kan batutuwa fiye da dubu 70 da ke da nasaba da ikon mallakar ilmi iri daban daban.

Xiao ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake ba da rahoton aiki a gun taron shekara-shekara a karo na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta sabon karo. Xiao kuma ya kara da cewa, a shekaru 5 da suka wuce, yawan manyan laifuffukan keta ikon mallakar ilmi da kotunan kasar a matakai daban daban suka sa aya ga yanke hukunci kansu ya karu da ninki sau 1.33 bisa na shekarar 1999 zuwa ta 2003. Yayin da suke daukar tsatsauran matakan murkushe laifuffukan keta ikon mallakar ilmi, kotunan kasar Sin sun kuma kara yaki da laifuffukan keta ikon mallakar ilmi a cikin batutuwan sayarwa da kuma kera kayayyakin jabu marasa inganci.(Tasallah)